| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Ghana ta karɓi 'yan Nijeriya da aka kora daga Amurka – Mahama
Yawancinsu ‘yan Nijeriya ne, yayin da ɗaya daga cikinsu ya kasance ɗan ƙasar Gambiya.
Ghana ta karɓi 'yan Nijeriya da aka kora daga Amurka – Mahama
Ghana ta samar da motar bas domin mayar da 'yan Nijeriyar gida / Reuters

Ghana ta tabbatar da isowar kashin farko na ‘yan Yammacin Afirka da aka kora daga Amurka a ƙarƙashin yarjejeniyar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Shugaba John Mahama, wanda ya tabbatar da hakan a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a fadar gwamnatin ƙasar Jubilee House ranar Laraba, ya ce mutum 14 ne jirgin sama ya kai ƙasar a wani ɓangare na yarjejeniyar.

Yawancinsu ‘yan Nijeriya ne, yayin da ɗaya daga cikinsu ɗan ƙasar Gambiya ne.

"Hukumomin Amurka sun yi mana tayin karɓar ‘yan wasu ƙasashe da ake so a fitar daga ƙasarsu sannan muka amince cewa za mu karɓi ‘yan Yammacin Afirka saboda dukkan ‘yan’uwanmu na Yammacin Afirka ba sa buƙatar izinin shiga ƙasarmu. Saboda haka idan sun zaɓi tafiya daga Amurka zuwa Accra ba sa buƙatar izinin shiga ƙasar. Saboda haka idan za ka dawo da ‘yan’uwanmu na Yammacin Afirka, ya yi daidai," in ji Shugaban ƙasar.

Ya ƙara da cewa Ghana ta taimaka wajen mayar da ‘yan Nijeriya ƙasarsu ta hanyar ba da motar bas da za ta kai su gida.

Ɗan ƙasar Gambiya kuwa, yana buƙatar a tattauna da ofishin jakadancin ƙasarsu domin samar da tikitin jirgin mayar da shi gida.

Shugaba Mahama ya jaddada cewa shigar Ghana lamarin yana daidai da yarjejeniyar ƙungiyar ECOWAS ta ‘yancin tafiya a cikin ƙasashenta wadda ta bai wa ‘yan ƙasashen ‘yancin iya shiga da kuma zama a cikin wasu ƙasashen Afirka ta Yamma ba tare da biza ba har na tsawon kwanaki 90.

“Afirka ta Yamma na da yarjejeniyar ‘yancin tafiye-tafiye, saboda haka ko wane ɗan Yammacin Afirka yana da ‘yancin zuwa Ghana kuma ya iya zaman kwanaki 90. Saboda haka idan suna dawowa da ‘yan’uwanmu, ba mu da wata matsala wajen karɓarsu,” in ji shi.

 

Rumbun Labarai
’Yansanda sun dakile harin ‘yanta'adda a Zamfara, sun gano gawarwaki fiye da 30
An gano mutum biyu da ake zargin sun kamu da cutar Ebola a Arewa maso Gabashin Nijeriya
INEC ta wallafa sunan Pantami a shafinta na ’yantakarar gwamna amma babu Gwarzo na Kano
Gwamnatin Nijeriya ta ƙaddamar da shirin tallafin kuɗi na N50,000 ga ’yan ƙasar da ke cikin talauci
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda Daesh 48, sun ƙwato makamai a jihohin Borno da Yobe
Wani sufeton ‘yansanda da fararen-hula 11 sun rasa rayukansu a wasu hare-haren ta’addanci a Kebbi
Tinubu ya kare matakin karɓo bashi daga waje, ya ce Nijeriya na buƙatar haɓaka tattalin arziki
NAFDAC ta lalata kayayyakin jabu da haramta amfani da su na Naira Biliyan 8 a Jihar Nasarawa
Dakarun Nijeriya sun ce sun kashe ‘yanta’adda 42 a arewa maso gabashin ƙasar
Nijeriya ta amince da biyan ma’aikatan gwamnatin tarayya naira 70,000 kudin sufuri duk wata
Mutane daga kasashe 120 na duniya ciki har da na Afirka 54 sun sayin hannayen jari a Matatar Dangote
'Yanayi mara kyau’ ne ya yi sanadin ɗaukewar numfashin masu hakar ma’adinai 37 a Nijeriya
Nijeriya za ta fara ƙera makamai masu yawa nan da shekara ɗaya — Christopher Musa
’Yansandan Zamfara sun kama matashin da ake zargi da yin kira don 'kai hari Enugu' a wani bidiyo
Tinubu ya nemi Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince ya karɓo bashin $20.51b da €1.04bn daga waje
Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da kisan Sheikh Masussuka, ya bayar da umarnin gudanar da bincike
’Yanbindiga sun kashe malamin addinin Musulunci a Nijeriya Sheikh Yahya Masussuka - ʼYansanda
Sheikh Bala Lau ya nemi a yi bincike kan ɗan agajin da ya nemi a ba su AK47 su kai hari
FBI ta kama mutane tara a Nijeriya da ake zargi da laifukan intanet, an ƙwace na’urori 53
EFCC ta kama ’yan China 14 da ɗan Nijeriya a masana’antun sarrafa lithium ba bisa ƙa’ida ba a Ogun