Turkiyya za ta karɓi baƙuncin COP31 bayan cim ma matsaya da Australia
Firaministan Australia Anthony Albanese ya ce Ministan Sauyin Yanayi Chris Bowen zai zama Shugaban taron COP don Tattaunawa, inda Turkiyya kuma za ta karbi baƙuncin COP31.
Turkiyya za ta karɓi baƙuncin taron sauyin yanayi na COP31 a shekara mai zuwa a garin hutu na Antalya da ke gaɓar tekun Bahar Rum, bayan Firaministan Australia Anthony Albanese ya sanar da janyewa takarar ƙasarsa.
“Abinda aka amince da shi shi ne cewa Ministan Sauyin Yanayi Chris Bowen na Australia ne zai shugabanci COP don Tattaunawa.”
“Taron da shugabancin COP zai tafi ga Turkiyya, sanna za a yi taro kafin fara Babban Taron na COP, musamman za a mayar da hankali kan ɗaukar nauyin sauyin yanayi a Pacific,” in ji Albanese yayin tattaunawa da tashar ABC Radio ta kasa ta Australia.
Ya bayyana yarjejeniyar a matsayin “babbar nasara ga Australia da Turkiyya”.
“Dokokin tarukan sauyin yanayi su ne cewa ana gudanar da su ta hanyar cim ma matsaya,” in ji shi. “Idan ba a cim ma matsaya ba, to damar ta suɓuce zuwa Bonn ta Jamus.”