Sudan ta yi Allah wadai da harin RSF wanda ya kashe yara mata 'yan makaranta
Harin wanda aka kai a wata makarantar sakandare da wata cibiyar kiwon lafiya a wani ƙauye na Sudan ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 17.
Gwamnatin Sudan ta yi Allah wadai da mummunan harin jirgin sama marar matuki wanda ya kashe aƙalla fararen-hula 17 a ƙauyen Shukeiri a Jihar White Nile, inda ta zargi dakarun RSF da kai harin
A cikin wata sanarwa, Firaminista Kamil Idris da mambobin gwamnati sun bayyana harin a matsayin abin ƙazanta.
“Firaminista, Farfesa Kamil Idris, da mambobin gwamnati suna bayyana baƙin cikinsu matuƙa da ta'aziyya kan waɗanda suka yi shahada a ƙauyen Shukeiri a Jihar White Nile, waɗanda aka ɗauki rayukansu a wannan watan mai albarka sakamakon harin jiragen sama marasa matuƙa da ‘yan tawaye kuma ‘yanta’addan RSF suka kai,” in ji wata sanarwa da Hukumar Labarai ta Sudan ta wallafa.
Gwamnatin ta ce harin ya faɗa kan fararen-hula a ƙauyen, kuma ta yi kira ga al'ummar duniya da su hukunta RSF saboda abin da ta bayyana a matsayin ayyukan azabtarwa da ake yi wa fararen-hula.
Haka kuma ta yi kira ga masu ruwa da tsaki na duniya da su sanya wannan runduna a matsayin ƙungiyar 'yan ta'adda.
‘Hari kan fararen-hula da gangan’
Harin ya faɗa kan makarantar sakandare da cibiyar lafiya a Shukeiri a ranar Laraba, ya kashe akalla mutane 17, mafi yawansu 'yan mata ɗalibai, kuma ya jikkata kusan wasu 10, a cewar jami'an kiwon lafiya.
Ƙungiyar Likitocin Sudan ta ce mamatan sun haɗa da ɗalibai mata, malamai da wani ma'aikacin lafiya. Kungiyar ta zargi RSF da kai harin kan muhimman wuraren fararen-hula da gangan.
“Wannan mummunan laifi na nuna ci gaba da keta haƙƙoƙi da RSF ke aikatawa a White Nile,” in ji ƙungiyar.
Ta ƙara da cewa an kai hari kan wasu wuraren fararen-hula a 'yan kwanakin nan, ciki har da ɗakin kwanan ɗalibai, tashar samar da wutar lantarki da unguwannin zama.
Sudan ta tsunduma cikin rikici tun Afrilun 2023 lokacin da rikici ya ɓarke tsakanin sojoji da dakarun Rapid Support Forces, wanda yaƙi ne da ya kashe dubban mutane kuma ya tilasta miliyoyi jama’a yin hijira.