Hukumar leƙen asiri ta ƙasar Afirka ta Kudu ta faɗa ranar Litinin cewa, fiye da mutane 25,000 aka mayar zuwa ƙasashensu a makonnin baya bayan nan, kafin gangamin da aka shirya na nuna ƙyamar baƙi. Har yanzu akwai da yawa da ke jiran barin ƙasar.
Wannan ficewa ta faru ne yayin da dubban mutane ke ƙoƙarin barin ƙasar saboda tsoron rashin tsaro bayan da ƙungiyoyin da 'yan ƙasa ke jagoranta suka fitar da wata sanarwa ba ta hukuma ba, suna umartar baƙi marasa takardu su bar ƙasar kafin 30 ga Yuni.
Gwamnatoci da dama, ciki har da na Nijeriya, Malawi, Ghana, Zimbabwe da Mozambique, sun shirya jiragen sama da bas-bas na don mayar da 'yan ƙasashensu bisa raɗin-kai, bayan makonni na zanga-zangar da ake yi don ƙyamar baƙi.
"Zuwa yanzu an mayar da fiye da mutane 25,000 'yan ƙasashen waje," in ji Hukumar Hadin Gwiwar Ayyukan Tsaro da Bayanan Leƙen Asiri ta Ƙasa (NATJOINTS), wadda ke kula da ayyukan tsaro da suka shafi zanga-zangar.
Ana ci gaba da aiwatarwa
Sabbin alƙaluma sun nuna ƙaruwa mai yawa daga makon da ya gabata, lokacin da hukumomi suka ce an shirya fitar da ‘yan Malawi 15,000. Aƙalla ‘yan Ghana 988 da kusan 'yan Nijeriya 600 sun tashi ta jirgin sama a farkon wannan watan.
"Wannan aiki ne da ake ci gaba da yi," in ji NATJOINTS, tana mai ƙara cewa an tura rukunoni na musamman, ciki har da tawagogin masu karnuna da reshen jiragen sama.
Ƙungiyoyin da ke adawa da shigowar baƙi ba bisa ƙa'ida ba sun goyi bayan wa'adin Talata da ba shi da izinin gwamnati, inda suke kira ga baƙin haure marasa takardu su tafi ko su fuskanci mummunan sakamako.
Sun kuma shirya jerin zanga-zanga a sassa daban-daban na ƙasar.
‘Yan Ethiopia, Mozambique da Malawi sun mutu
Ana hakan, wasu gungun masu fafutuka suna bi gida-gida suna gaya wa baƙin haure su tafi, ko su nuna takardunsu na zama.
NATJOINTS ta ce wannan "mugun ra'ayin adawa da baƙi" ya janyo mutuwar mutane huɗu.
'Yan sanda sun shaida wa AFP cewa waɗanda suka mutu sun haɗa da mutane biyu daga Mozambique, ɗan Habasha guda ɗaya da ɗan Malawi guda.
Firgicin tsaro ya sa dubban baƙin haure taruwa cikin sansanoni na wucin-gadi a kudu-maso-gabas na birnin Durban, cibiyar yawon buɗe-ido ta Cape Town, da kuma babban birnin hada-hadar kuɗi, Johannesburg, suna masu jiran fito zuwa ƙasashensu.
Matsanancin rashin aikin-yi
Afirka ta Kudu, wadda ta kasance daɗaɗɗiyar matattara ga ma'aikatan ƙasashen waje, a yanzu tana fama da rashin aikin-yi na fiye da kashi 30%.
Ƙasar na kuma da tarihin maimaituwar rikice-rikice na adawa da baƙi, wanda sau da yawa ake dangantawa da zargin cewa baƙin haure na karɓe ayyukan ‘yanƙasa.
Rikice-rikice na baya da aka yi saboda baƙin haure marasa takardu, sun haifar da mace-mace, wanda ya halaka mutane 62 a tarzomar 2008.










