| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
An daƙile makami mai linzami na Iran a kan hanyarsa ta kutsawa Turkiyya
Tarkacen makamin sun faɗa a yankin Gundumar Sahinbey na Jihar Gaziantep a kudu-maso-gabashin Turkiya. Mahukunta sun ce ba a samu asarar rai ko raunuka ba.
An daƙile makami mai linzami na Iran a kan hanyarsa ta kutsawa Turkiyya
An daƙile makami mai linzami na Iran a kan hanyarsa ta kutsawa Turkiyya / TRT World
11 awanni baya

Hukumomin Turkiya sun ce tsarin kariyar sama na NATO ya samu nasarar daƙile wani makami mai linzami da aka harba daga Iran da ke kan hanyar zuwa Turkiya, lamarin da ya zama karo na biyu na shigar makaman Iran cikin sararin samaniyar Turkiya a cikin mako guda.

A cewar Ma'aikatar Tsaron Kasa ta Turkiya a ranar Litinin, an gano roket ɗin a saman Gabashin Tekun Bahar Rum kuma an daƙile shi ta hanyar tsarin kariyar sama da na makaman roket na kawance.

Tarkacen makamin sun faɗa a yankin Gundumar Sahinbey na Jihar Gaziantep a kudu-maso-gabashin Turkiya. Mahukunta sun ce ba a samu asarar rai ko raunuka ba.

Ankara ta yi gargadi kan ka da a ƙara tsananta rikici

Burhanettin Duran, Shugaban Harkokin Sadarwa na Turkiyya, ya ce "an tsayar da makamakin a kan lokaci kuma an kawar da barazanarsa" da kayan aikin tsaron NATO yayin da yake gabatowa Turkiyya.

Ya ce ma'aikatun gwamnati sun sa idanu sosai kan lamarin tun daga farko kuma suka kunna matakan tsaro da kariya da suka dace.

"Dukkan sassan da abin ya shafa, musamman Ma'aikatar Tsaron Kasa, suna aiki cikin cikakkiyar hadin gwiwa," in ji Duran, yana jaddada cewa ƙwarewar ƙasa da azama wajen kare sararin samaniya da tsaron iyakokin Turkiya sun kasance a mataki mafi girma.

Duran ya kuma yi gargadi kan kada a ƙara tsananta rikici a yankin, yana roƙon dukkan bangarori — musamman Iran — da su guje wa matakai da za su iya zama barazana ga zaman lafiyar yankin ko sanya fararen hula cikin haɗari.

"Yana da matuƙar muhimmanci k ada tashin hankali a yankin ya ƙara ƙaruwa kuma ka da rikicin ya yadu zuwa wani babban yanki," in ji shi.

Ya kuma yi kira ga 'yan ƙasa da kafafen watsa labarai su dogara kawai ga sanarwar hukuma su guji yaɗa bayanai marasa tabbaci waɗanda za su iya janyo firgici a tsakanin jama'a ko yaɗa bayanan ƙarya.

Daƙile wannan makami ya biyo bayan wani irinsa da ya faru a makon da ya gabata, wanda aka harba daga Iran zuwa sararin samaniyar Turkiyya, abin da ke ƙara nuna damuwa cewa rikicin da ke faɗaɗa a Gabas ta Tsakiya na iya watsuwa cikin yankunan NATO.