| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Nijeriya ta yi alƙawarin tallafa wa 'yan ƙasar 271 da suka dawo daga Afirka ta Kudu
Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Dakta Bernard Doro ya ce gwamnati na ci gaba da jajircewa wajen kare mutunci da walwalar 'yan Nijeriya a duk inda suke.
Nijeriya ta yi alƙawarin tallafa wa 'yan ƙasar 271 da suka dawo daga Afirka ta Kudu
Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Dakta Bernard Doro ya ce gwamnati na ci gaba da jajircewa wajen kare mutuncin 'yan Nijeriya a duk inda suke.

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yi alƙawarin tallafa wa 'yan ƙasar 271 da suka dawo daga Afirka ta Kudu, tana mai tabbatar musu da cewa za ta taimaka musu wajen sake shiga cikin al'umma da kuma farfaɗo da rayuwarsu.

Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Dakta Bernard Doro ya ce gwamnati na ci gaba da jajircewa wajen kare mutunci da walwalar 'yan Nijeriya a duk inda suke.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, ya ce waɗanda suka dawo za su samu tallafi domin su sake gina rayuwarsu cikin mutunci.

Doro ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta ci gaba da ba da taimako ga 'yan Nijeriya da suka dawo daga ƙasashen waje bayan sun fuskanci ƙalubale.

Ya jaddada cewa ba za a yi watsi da wani ɗan ƙasa ba, yana mai cewa kowane mai dawowa gida ya cancanci damar sake fara rayuwa mai amfani.

Ya bayyana cewa shirin sake tsugunar da masu dawowar bai tsaya kan tarbarsu a filin jirgin sama kawai ba.

Ya ce shirin ya haɗa da tantance su, ba su tallafin jinƙai, tura su zuwa hukumomin da suka dace, da kuma samar musu da damar shiga shirye-shiryen dogaro da kai.

Ministan ya ce waɗanda suka dawo ba masu laifi ba ne, sai dai sun yanke shawarar komawa gida ne bayan sun fuskanci mawuyacin hali yayin neman halastacciyar hanyar samun abin rayuwa a Afirka ta Kudu.

Haka kuma ya yi kira ga gwamnatocin jihohi, kamfanoni masu zaman kansu, ƙungiyoyin ci gaba, shugabannin al'umma da iyalai su mara wa gwamnati baya wajen tallafa musu.

Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira, 'Yan Ci-rani da Mutanen da Rikici ya Raba da Muhallansu (NCFRMI), wadda ke jagorantar shirin karɓar da sake tsugunar da masu dawowar, ta ce za ta ci gaba da sa ido kan farfaɗo da rayuwarsu ta hanyar shirye-shiryen koyon sana'o'i da sauran tsare-tsaren samar da abin dogaro.

Daraktar Harkokin 'Yan Ci-rani ta hukumar, Ambasada Catherine Udida, ta kuma bayyana cewa ana sa ran wasu ƙarin rukunan masu dawowa za su iso cikin makonni masu zuwa.

Wasu daga cikin waɗanda suka dawo sun buƙaci ƙarin tallafi daga gwamnati. Adeyemo Place ya ce ya dawo gida ba tare da kusan komai ba, bayan da ya sayar da kadarorin da ya tara cikin fiye da shekara goma kan farashi mai rahusa.

Shi kuwa John Okeke ya buƙaci gwamnatin tarayya ta ɗauki batun hare-haren ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu da muhimmanci, yana mai cewa 'yan Nijeriya masu bin doka ba su cancanci irin yadda aka yi musu mu'amala ba.

Rukunin mutane 271 na baya-bayan nan sun isa filin jirgin sama na Legas da misalin ƙarfe 10:40 na safiyar Talata a cikin jirgin kamfanin Air Peace daga Johannesburg.

Dawowarsu wani ɓangare ne na shirin gwamnatin tarayya na dawo da 'yan Nijeriya da suka zaɓi komawa gida sakamakon ƙaruwar rashin jituwar da ta shafi baƙin haure a Afirka ta Kudu.

Rumbun Labarai
Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya ta kama wasu mutane da kudade da ake zargin kuɗin fansa ne
'Yansandan Nijeriya sun kama mutum biyu kan zargin kashe Danshagamu a Kano
Nijeriya ta naɗa sabon kwamandan yaƙi da ƙungiyar ta’addanci ta Boko Haram
NEMA ta karɓi ’yan Nijeriya 180 da aka mayar da su gida daga Libya
Sojojin Nijeriya sun kama wasu da ake zargin masu kai wa ’yanta’adda kayayyaki ne a Jihar Yobe
FIFA ta tura tawaga zuwa Nijeriya don gano ko gwamnati ta tsoma baki a murabus ɗin shugabannin NFF
INEC za ta ƙaddamar da na’urar bibiyar shirye-shiryen zaɓe kai-tsaye
An  kashe mutum 12, an jikkata 2 a sabon harin da Boko Haram ta kai wani ƙauye a Adamawa ta Nijeriya
‘Yanbindiga sun kashe mutum 10, sun sace 40 a wani ƙauyen Sokoto
Gwamnatin Jihar Filato a Nijeriya ta rufe makarantu saboda ɓarkewar cutar mashaƙo
NDC ta yi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa kan ba ta da ’yan takarar gwamna a jihohin Nijeriya 12
Sojojin Nijeriya sun ceto mutum 36 da aka sace a kasar, sun kuma halaka ’yanta’adda da dama
‘Yanbindiga sun kashe mutum biyar tare da jikkata uku a wasu ƙauyukan Sokoto
Shari'ar Tinubu a Amurka ta neman haƙƙi ce ba ta laifi ba ce— Fadar Shugaban ƙasa
Darakta Janar na DSS ya umarci jami'ansu da kar su kama kowa yayin da farar-hula suka samu sabani
Nijeriya ta musanta zargin goyon bayan yunƙurin 'juyin mulki' a Nijar
Hukumar DSS ta Nijeriya ta ƙwato bindigogi 676 da harsasai 332,000
INEC za ta yi zaɓen gwaji na Shugaban Ƙasa gabannin zaɓen 2027 na Nijeriya
Ɓarayin daji sun ƙaƙaba harajin naira miliyan 40 kan mazauna wani gari a Sokoto
An lalata makarantu fiye da 1000, an kashe malamai 2,295 a Arewa maso Gabashin Nijeriya - Hukumomi