| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Ɗanyen man da Nijeriya ke samarwa ya kai matakin da ya fi yawa tun watan Yunin 2020
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito cewa ƙididdigar da hukumar da ke sa ido a kan fannin haƙo man fetur ranar Lahadian ta ce an samu samu ƙarin ne sakamakon daidaituwar aiki da ingancin bututun mai.
Ɗanyen man da Nijeriya ke samarwa ya kai matakin da ya fi yawa tun watan Yunin 2020
Tsohon Hoto: Matatar mai Dangote na cikin ababe ci-gaban da aka samu a masana'antar man Nijeirya cikin 'yan shekarun nan

Adadin ɗanyen man da Nijeriya ke samarwa ya kai mataki mafi ƙololuwa cikin sama da shekara shida a watan Yuni, inda ya ɗara kason da ƙungiyar OPEC ta ware mata.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito cewa ƙididdigar da hukumar da ke sa ido a kan fannin haƙo man fetur ranar Lahadian ta ce an samu samu ƙarin ne sakamakon daidaituwar aiki da ingancin bututun mai.

Ƙasar da ta fi samar da mai a nahiyar Afirka ta samar da gangar ɗanyen mai miliyan 1.56 a ko wace rana a watan da ya gabata, adadin da ya zarce ganganr mai miliyan 1.5 a ko wace rana da OPEC ta bai wa Nijeriya damar fitarwa.

Kazalika alƙallumna sun nuna cewa ƙasar ta ta cim ma kashi 104 cikin 100 na biyayya ga doka.

Idan aka haɗa da wani nau’in mai (condensates) da ba ya ƙarƙashin ikon kason OPEC, adadin man da Nijeriya ta samar ya kai kimanin gangar mai miliyan 1.735 a ko wace rana a watan Yuni, adadin da baiu wuce gangar mai miliyan 1.700 a ko wace rana ba a watan Mayu.

Reuters ya ruwaito cewa wannan shi ne wata na huɗu a jere da adadin man ke ƙaruwa.

Adadin man da ƙasar ta samar a watan Yuni shi ne adadi mafi yawa da ƙasar ta samar tun watan Afrilun shekarar 2020, adadi mafi yawa cikin watanni 74.

Daidaituwar aiki a wuraren haƙar mai da kuma rashin toshe ko wane muhimmin bututun mai sun taimaka wajen ƙara lokacin haƙar mai da kuma yawan man da ake fitarwa, in ji alƙalluman.