Helikwaftan sojin Iran ya yi hatsari a lardin Isfahan, mutum huɗu sun mutu

Wannan shi ne hatsarin jirgin sama na biyu cikin ƙasa da mako ɗaya a Iran, bayan jirgin yaƙi ƙirar F-4 ya faɗi kusa da Hamedan, inda ya kashe ɗaya daga cikin matuƙa jirgin.

By
Matukin jirgin da mataimakinsa sun mutu tare da da fararen hula biyu da ke aiki a shagunan kasuwa. / AA

Wani helikwaftan sojin Iran ya faɗi a yankin Dorcheh na lardin Isfahan na Iran ranar Talata, inda ya kashe mutum huɗu, kamar yadda kafofin watsa labaran ƙasar suka ruwaito.

Rahotannin wucin-gadi sun ce helikwaftan ya faɗi cikin wata kasuwar kayayyakin marmari da kayayyakin miya ne, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Mehr News Agency wanda ƙasar Iran ke da ƙwarya-kwaryar iko a kansa ya ruwaito.

Helikwaftan yana kan hanyarsa ta zuwa aikin koyarwa ne a lokacin da ta faɗi, in ji kamfanin dillancin labaran, yana mai ƙarawa da cewa mai tuƙa jirgin da mataimakinsa sun mutu tare da fararen-hula biyu a shagunan kasuwa.

Kawo yanzu dai ba a bayyana abin da ya yi silar faɗuwar jirgin ba.

Wannan shi ne faɗuwar jirgi na biyu cikin ƙasa da mako ɗaya a Iran. Jirgin yaƙi ƙirar F-4 ya faɗi ranar Alhamis kusa da birnin Hamedan a yammacin Iran, inda ya kashe ɗaya daga cikin masu tuƙa jirgin.