Jan hankalin gwamnatin Nijeriya ga 'yan ƙasar masu shiga yaƙi a wasu ƙasashen ƙetare
Sanarwar ta ce ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fara ɗaukar matakai don magance wannan matsala.
Kwanaki kaɗan bayan wasu jaridun Nijeriya sun wallafa labarin kashe wasu ’yan ƙasar a yaƙin Rasha da Ukraine waɗanda suka shiga yaƙin a matsayin sojojin haya, gwamnatin Nijeriyar ta fitar da wata sanarwa inda ta gargadi ’yan ƙasar da su guji shiga yaƙin da ake yi a ƙasashen ƙetare.
Ministan Harkokin Wajen Nijeriya Yusuf Tuggar ya bayyana damuwarsa kan yadda ake ci gaba da samun ƙaruwar ’yan ƙasar da suke shiga yaƙe-yaƙe da ake yi a wasu ƙasashen duniya, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Kimiebi Ebienfa ya bayyana a sanarwar da ya fitar ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fara ɗaukar matakai don magance wannan matsala.
Ministan harkokin wajen kasar ya ce kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka bayyana cewa ’yan Nijeriya suna amincewa da buƙatar da aka gabatar musu ne bayan an yi musu shigo-shigo ba zurfi, da yi musu alkawuran ba su albashi mai tsoka da ba su ayyukan dindindin da damarmakin karatu da sauransu.
Ya ce ’yan ƙasar da dama sun faɗa wannan tarkon kuma an tura su fagen daga don yin yaƙi bayan an tilasta musu sanya hannu kan yarjejeniyar shiga aikin soja.
Sanarwar ta ce a lokauta da dama waɗanda suke faɗawa wannan matsala bisa tilas suna sanya hannu a yarjejeniya da aka rubutu a wani harshe da ba sa ganewa, ba tare da an yi musu cikakken bayanin da ya kamata ba kuma sai a ƙwace takardun tafiye-tafiyensu da zarar sun isa ƙasar.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta gargaɗi ’yan ƙasar kan su guji shiga duk wata yarjejeniya ta barin ƙasar don shiga wasu yaƙe-yaƙe da ake yi a wasu ƙasashen duniya.
Sannan ma’aikatar ta sanar da cewa duk wani ɗan Nijeriya da ya zaɓi ya je ya shiga wani yaƙi da ake yi a wata ƙasa ta ƙetare, to duk abin da ya faru da shi, shi ya jawo wa kansa.
Galibi matasan da suke son barin Nijeriya ta kowane irin hali suna kafa hujja da rashin aikin yi da matsalar tsaro da talauci da rashin abubuwan more rayuwa da sauransu.
Sannan suna cewa suna zuwa ƙasashen ƙetare ne don neman buɗi a rayuwarsu da neman sabbin damarmaki musamman na ayyuka waɗanda ake biyan albashi mai tsoka.
Ministan Harkokin Wajen Nijeriya ya buƙaci iyaye da shugabannin al’umma da su riƙa jan hankalin matasa kan su guji jefa kansu cikin hatsari a ƙoƙarin da suke na neman barin ƙasar ta kowane irin hali.
Ya ce idan ya zama dole sai mutum ya bar ƙasar don neman aiki ko karatu, to kamata ya yi ya bi ta hanyoyin da hukuma ta tanada. Minista Tuggar ya kuma nemi mutane su dinga kai wa hukumomi rahoton masu ƙokarin fitar da mutane ƙasashen ƙetare waɗanda ba su yarda da take-takensu ba.