Jan hankalin gwamnatin Nijeriya ga 'yan ƙasar masu shiga yaƙi a wasu ƙasashen ƙetare
NIJERIYA
3 minti karatu
Jan hankalin gwamnatin Nijeriya ga 'yan ƙasar masu shiga yaƙi a wasu ƙasashen ƙetareSanarwar ta ce ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fara ɗaukar matakai don magance wannan matsala.
Jan hankalin gwamnatin Nijeriya ga 'yan ƙasar masu shiga yaƙi a wasu ƙasashen ƙetare / Reuters
16 Fabrairu 2026

Kwanaki kaɗan bayan wasu jaridun Nijeriya sun wallafa labarin kashe wasu ’yan ƙasar a yaƙin Rasha da Ukraine waɗanda suka shiga yaƙin a matsayin sojojin haya, gwamnatin Nijeriyar ta fitar da wata sanarwa inda ta gargadi ’yan ƙasar  da su guji shiga yaƙin da ake yi a ƙasashen ƙetare.

Ministan Harkokin Wajen Nijeriya Yusuf Tuggar ya bayyana damuwarsa kan yadda ake ci gaba da samun ƙaruwar ’yan ƙasar da suke shiga yaƙe-yaƙe da ake yi a wasu ƙasashen duniya, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Kimiebi Ebienfa ya bayyana a sanarwar da ya fitar ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fara ɗaukar matakai don magance wannan matsala.

Ministan harkokin wajen kasar ya ce kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka bayyana cewa ’yan Nijeriya suna amincewa da buƙatar da aka gabatar musu ne bayan an yi musu shigo-shigo ba zurfi, da yi musu alkawuran ba su albashi mai tsoka da ba su ayyukan dindindin da damarmakin karatu da sauransu.

Ya ce ’yan ƙasar da dama sun faɗa wannan tarkon kuma an tura su fagen daga don yin yaƙi bayan an tilasta musu sanya hannu kan yarjejeniyar shiga aikin soja.

Sanarwar ta ce a lokauta da dama waɗanda suke faɗawa wannan matsala bisa tilas suna sanya hannu a yarjejeniya da aka rubutu a wani harshe da ba sa ganewa, ba tare da an yi musu cikakken bayanin da ya kamata ba kuma sai a ƙwace takardun tafiye-tafiyensu da zarar sun isa ƙasar.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta gargaɗi ’yan ƙasar kan su guji shiga duk wata yarjejeniya ta barin ƙasar don shiga wasu yaƙe-yaƙe da ake yi a wasu ƙasashen duniya.

Sannan ma’aikatar ta sanar da cewa duk wani ɗan Nijeriya da ya zaɓi ya je ya shiga wani yaƙi da ake yi a wata ƙasa ta ƙetare, to duk abin da ya faru da shi, shi ya jawo wa kansa.

Galibi matasan da suke son barin Nijeriya ta kowane irin hali suna kafa hujja da rashin aikin yi da matsalar tsaro da talauci da rashin abubuwan more rayuwa da sauransu.

Sannan suna cewa suna zuwa ƙasashen ƙetare ne don neman buɗi a  rayuwarsu da neman sabbin damarmaki musamman na ayyuka waɗanda ake biyan albashi mai tsoka.

Ministan Harkokin Wajen Nijeriya ya buƙaci iyaye da shugabannin al’umma da su riƙa jan hankalin matasa kan su guji jefa kansu cikin hatsari a ƙoƙarin da suke na neman barin ƙasar ta kowane irin hali.

Ya ce idan ya zama dole sai mutum ya bar ƙasar don neman aiki ko karatu, to kamata ya yi ya bi ta hanyoyin da hukuma ta tanada. Minista Tuggar ya kuma nemi mutane su dinga kai wa hukumomi rahoton masu ƙokarin fitar da mutane ƙasashen ƙetare waɗanda ba su yarda da take-takensu ba.

Rumbun Labarai
'Yanta'addan ISWAP sun kashe sojojin Nijeriya 14 a hare-hare biyu
Tinubu ya ba da umarnin fitar da kudi nan-take don gyara kayan aikin sararin samaniyar Nijeriya
Nijeriya ta tara fiye da naira tiriliyan biyu daga harajin VAT a wata uku na karshen 2025 – NBS
'Yanbindiga sun raba fiye da mutum 300,00 da gidajensu a jihar Neja – Gwamna Bago
Ramadan: INEC ta sauya ranakun zaɓen 2027
An kashe aƙalla mutum 25 a wani hari da ake zargin Boko Haram da kai wa a Jihar Adamawa a Nijeriya
Hare-haren ƙungiyoyin 'yanta'adda kan iyakokin Nijar, Benin da Nijeriya na ƙaruwa: Bincike
Ƙalubalen da ke gaban sabon Sufeto Janar na 'yansandan Nijeriya
Gwamnatin Nijeriya ta musanta zargin biyan kudin fansa don ceto daliban Jihar Neja
'Yansandan Nijeriya sun kashe ɓarayin daji tare da kama mai safarar makamai a Kaduna
Tarayyar Afirka ta nemi a 'ɗauki mataki' bayan an kashe gomman mutane a Zamfara a Nijeriya
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda 25 masu alaƙa da Daesh a jihar Borno
NDLEA ta kama matar da ta kifa ƙwarya a matsayin cikin bogi don ɓoye ƙwayoyi
Jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta lashe zaɓukan cike gurbin da aka gudanar a Kano
Nijeriya: 'Yanbindiga sun kashe mutum 50 da garkuwa da wasu da dama a Jihar Zamfara
Hukumar NCDC ta Nijeriya ta tabbatar da samun mutum 318 ɗauke da zazzaɓin Lassa da mutuwar mutum 70
Gobara ta ƙona shaguna aƙalla 50 a Kasuwar Fatima Simra a Kanon Nijeriya
'Yansanda sun tabbatar da mutuwar mutum 33 a harin Kebbi
Dakarun Nijeriya sun kama mai 'kai wa Boko Haram jirage marasa matuƙa'
Mutane da dama sun rasa rayukansu a hare-haren Lakurawa a Jihar Kebbi a Nijeriya