Ghana ta yi wa jakadanta a Nijeriya kiranye kan zargin maguɗin zaɓe
Matakin ya biyo bayan zarge-zargen sayen ƙuri'u ne yayin zaɓen fid da gwani na 'yan majalisu a Jam'iyyar NDC.
Shugaba John Mahama na Ghana ya yi wa jakadan ƙasar a Nijeriya, Baba Ahmed, kiranye bisa zargin hannu a maguɗin zaɓe a zaɓen fid da gwani na ‘yan majalisu a mazaɓar Ayawaso East.
Wata sanarwa da fadar Shugaban ƙasar Ghana ta fitar a Accra ta bayyana cewa an yi Ahmed, wanda ya kasance mai neman takara, kiranye ne sakamakon rawar da ake zargin ya taka a maguɗin zaɓe a matsayinsa na jam’in gwamnati.
Sanarwar ta ce kiranye zai yi aiki ne nan-take, kuma an ɗauki matakin ne domin kauce wa duk wani tunanin rashin adalci ko kuma saɓa wa dokar ɗa’ar ma’aikata ga waɗanda aka bai wa muƙaman siyasa.
Ta jaddada cewa ci gaba da zamansa a ofishin abu ne da ba zai yiwu ba a irin wannan yanayi.
An zargi masu neman takara a zaɓen fid da gwani da laifin sayen ƙuri’u.