A tarihi an ga masu sha'awar ƙwallon ƙafa sun daɗe suna yin wata sara, a tsawon shekaru, amma ba a taɓa ganin wadda ta daɗe kuma ta girma kamar gashin kan Frank Ilett ba.
A watan Oktoban 2024, wani masoyin Manchester United daga Oxford ya yi rantsuwa, kuma tun lokacin bai karya alƙawarin da ya yi ba har yau.
Ilett ya shelanta cewa ba zai aske gashinsa ba har sai United ta ci wasanni biyar a jere. Abin da ya fara a matsayin wasa a kafafen sada zumunta ya zama alamar rashin tagomashin kulob ɗin.
Yau kimanin kwanaki 500 bayan nan, gashinsa ya zama cunkus dinsa kuma yanzu ya kai kimanin tsayin santimita 25 ba tare da aske shi ba.
A lokacin, ya wallafa saƙo yana tambayar masu bibiyar sa su kaɗa ƙuri’a kan lokacin da zai sake aski: 2024, 2025, ko 2026. Daga mutane 27,000 da suka amsa, kashi 90% sun zaɓi 2026. A wancan lokacin abin ya yi kama da munana fata, amma yanzu ya zama tamkar bushara.
An saka wa saƙon ƙalubalen suna “The United Strand”, kuma ya samu karɓuwa. Ilett yana wallafa saƙo kullum-kullum game da halin da yake ciki, yana sharhi kan wasa, yayin da gashinsa ke ƙaruwa.
Sumar Ilett tasa ta janyo ya samu mabiya a intanet sama da miliyan 2.3, kuma ga farin jini wajen manyan kafafen labaran wasanni. Watsa bidiyo kai-tsaye da ya yi yayin wasan Talata na United da West Ham, ya samu masu kallo fiye da 100,000 a lokaci guda.
Lokacin wasan an yi zaton sumar wahalar Ilett za ta zo ƙarshe.
United sun shiga wasan da West Ham bayan nasarori huɗu a jere — mafi kyawun jerantawar da suka samu cikin tsawon lokaci. Har ta kai Ilett ya yayyafa ruwa a kansa yana shirye-shiryen yin aski da zarar United ta samu nasara ta biyar.
Sai dai wasn ya zo da sammatsi sabod an tashi ne da ci 1–1, wanda ke nufin jeranta nasarar United ta zo ƙarshe. Gashin Ilett zai ci gaba da taruwa.
Manchester United za ta buga wasa na gaba da Everton a ranar 23 ga Fabrairu. Kuma wata dama ce da za ta fara sabon jere.










