Ɗaruruwan yara sun isa sansanin gudun hijira ba tare da iyayensu ba bayan tsere wa rikicin Darfun

UNICEF ta rubuta adadin yara 354 da suka isa sansanin gudun hijira na Tawila ba tare da ‘yan uwansu ko iyayensu ba, kusan kilomita 70 daga yammacin Al Fasher a tsakanin 26 ga Oktoba zuwa 22 ga Nuwamba.

By
Rahotanni sun ce yara da dama sun isa sansanin da yunwa a tattare da su kuma jikinsu duk ƙashi saboda sun rame

Ɗaruruwan yara sun isa sansanin ’yan gudun hijira ba tare da iyalansu ba yayin da dubban mutane suka tsere daga tashin hankali a birnin Al Fasher na Sudan a cikin watan da ya gabata, kuma a kowace rana ana samun ƙarin yara da suka rabu da iyalansu, in ji jami’ai.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutane 100,000 sun tsere daga Al Fasher a yammacin Darfur tun daga ƙarshen Oktoba a lokacin da dakarun Rapid Support Forces (RSF) suka sake kwace Al Fasher daga hannun sojojin Sudan.

UNICEF ta rubuta adadin yara 354 da suka isa sansanin gudun hijira na Tawila ba tare da ‘yan uwansu ko iyayensu ba, kusan kilomita 70 daga yammacin Al Fasher a tsakanin 26 ga Oktoba zuwa 22 ga Nuwamba. Jami’an sun ce iyayensu sun ɓace ko an kama su ko an kashe su yayin tafiya.

Asusun Kula da Ƙananan da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF ta ce a cikin wata daya da ya gabata an sake haɗa yara 84 da iyalansu, yawanci a Tawila inda kungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa da dama ke ba da tallafi ga mutanen da rikicin Al Fasher ya shafa, babban birnin Darfur ta Arewa da RSF ta karɓe a watan da ya gabata.

Hukumar Norwegian Refugee Council ta ce aƙalla yara 400 sun isa Tawila ba tare da iyayensu ba.

Wasu sun isa sansanin ne tare da taimakon ’yan uwa na nesa, makwabta da baƙi waɗanda ba su so su barsu su kaɗai a sahara ko a Al Fasher, in ji Mathilde Vu, manajar fafutuka ta NRC, a ranar Alhamis.

“Yawancin yara sun iso da alamun yunwa a fili, sun zo a rame. Jikinsu duk ƙashi, suna fama da rashin ruwa,” kamar yadda ta bayyana, sannan ta ƙara da cewa wasu suna nuna alamun matsalar ƙwaƙwalwa ciki har da tashin hankali, rashin magana, yin kuka ko da yaushe, inda suka ce suna mafarkai masu tayar da hankali.

‘Ruɗani, rashin abinci da kuma rashin ruwa a jiki’

Raba mutane da muhallansu a baya-bayan nan ya fara ne lokacin da tashin hankalin RSF ya kashe daruruwan mutane a Al Fasher, wanda shi ne wuri na ƙarshe da sojojin Sudan na ke riƙe da shi a Darfur.

Yaƙi tsakanin RSF da sojoji ya fara a 2023, lokacin da taƙaddama ta ɓarke tsakanin tsoffin abokan ƙawancen biyu da aka tsara za su jagoranci canjin dimokuradiyya bayan tashin hankalin 2019.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce faɗa ya kashe aƙalla mutane 40,000 ya kuma tilasta wa mutane miliyan 12 yin ƙaura a Sudan. Sai dai ƙungiyoyin agaji suna cewa adadin mamatan na iya zama fiye da haka.

Sheldon Yett, wakilin UNICEF a Sudan, ya bayyana yaran da ke isa sansanin a matsayin waɗanda ke cikin ruɗani da rashin abinci da rashin ruwa a jiki”

Ko da yake ma’aikatan agaji sun ba yara tallafi ta hanyar bayar da shawarwarin gyaran tunani, wasu har yanzu suna barci a ƙasa kuma kusan ba sa samun abinci fiye da sau ɗaya a rana, in ji Vu na NRC.

“Mutane na jin yunwa, suna jin ƙishirwa, suna buƙatar ilimi, suna buƙatar taimako da kulawa, suna buƙatar tallafin zamantakewa da na tunani kuma dole mu ba su yanzu ba tare da jiran zaman lafiya ya dawo Sudan ba,” kamar yadda Vu ta ƙara da cewa.

A farkon wannan watan, RSF ta amince da yarjejeniyar tsagaita ta jinkai da wata ƙungiyar masu shiga tsakani da Amurka ke jagoranta ta bayar, amma sojojin Sudan sun ce RSF dole ta janye gaba ɗaya daga yankunan farar-hula kuma ta ajiye makamai.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce a baya yana shirin matsawa don kawo ƙarshen yakin basasa a Sudan.