| Hausa
TURKIYYA
1 minti karatu
Jami’an Sojin Ruwa 30 na Saudiyya sun kammala karɓar horo a kamfanin tsaron Turkiyya, Baykar
Masu tuƙa jiragen saman 15 da masu gyara 15 sun kammala horaswa a wani ɓangare na wani aikin haɗin gwiwa da ya ƙunshi jirage yaƙi mara matauƙa na Bayraktar AKINCI.
Jami’an Sojin Ruwa 30 na Saudiyya sun kammala karɓar horo a kamfanin tsaron Turkiyya, Baykar
Jami'an sun haɗa da masu taƙar jiragen sama 15 da masu koyan kaninci da gyaran lataroni 15

Kamfanin tsaron Turkiyya Baykar ya sanar da cewa jami’ai 30 daga Rundunar Sojin Ruwa ta Masarautar Saudiyya sun kammala horo bayan sun kammala shirin horarwa a cibiyar kamfanin da ke arewa maso yammacin Turkiyya.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, kamfanin ya ce rukunin jami’an ya ƙunshi matuƙan jiragen sama 15 da kuma masu horaswa kan aikin gyaran na’urorin injina da na lantarki 15, waɗanda suka kammala shirye-shiryensu a Cibiyar Horarwa da Gwajin Jiragen Sama ta Baykar da ke Çorlu.

A shekarar 2023, Baykar da Ma’aikatar Tsaron Saudiyya sun sanya hannu kan yarjejeniyar fitar da kaya da haɗin gwiwa kan jirgin yaƙi mara matuƙi na Bayraktar AKINCI (UCAV).

A ƙarƙashin yarjejeniyar, za a ƙara jiragen yaƙi marasa matuƙi na Bayraktar AKINCI cikin jerin kayan aikin Sojojin Saudiyya.

Baykar zai kuma samar da horo, tallafin fasaha da kuma ayyukan samar da kayan aiki a matsayin wani ɓangare na haɗin gwiwar.