| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Galatasaray ta doke Juventus da ci 5-2 a Gasar Zakarun Turai
Babar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Turkiyyar ta doke ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Italiyar a zagaye na farko na karawarsu a gasar Zakarun Turai.
Galatasaray ta doke Juventus da ci 5-2 a Gasar Zakarun Turai
Ɗan wasan Nijeriya Victor Osimhen ne ya yi silar ƙwallaye biyu daga cikin biyar da Galatasaray ta zura a ragar Juve / Reuters
16 awanni baya

Galatasaray ta samu gagarumar nasara da ci 5-2 a kan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus mai ‘yan wasa 10 a zagaye na farko na karawarsu a gasar Zakarun Turai, inda Noa Lang da Gabriel Sara suka taka rawar gani a wasan.

Sara ne ya fara zura ƙwallo a ragar masu masaukin baƙi a ranar Talata minti 15 da fara wasa, amma Juventus ta rama nan-take ta hanyar Teun Koopmeiners.

Koopmeiners ya zura ƙwallo na biyu minti 32 da fara wasa da wani ƙwallon da ya buga daga wajen gidan Galatasaray, lamarin da ya sa ƙungiyar ta Italiya ta shige gaban ƙungiyar ta Turkiyya.

Galatasaray ta rama bayan an dawo daga hutun rabin lokaci yayin da Lang ya zura ƙwallo a raga bayan ƙoƙarin zura ƙwallon Baris Alper Yilmaz ya ci tura.

Kana ƙungiyar ta Turkiyya ta ƙara ƙwallo a lokacin Davinson Sanchez ya zura wata ƙwallon da Sara ya turo cikin raga.

‘Yanwasan Juventus sun ragu zuwa 10 minti 67 da fara wasa a lokacin da aka bai wa Juan Cabal jan kati domin ya samu katin gargaɗi biyu.

Lang ya ƙara zura ƙwallo a ragar Juve minti 75 da fara wasa, kafin Sacha Boey ya ƙara ƙwallo na biyar minti huɗu kafin a kammala wasan.

Za a buga zagaye na biyu na wasan a birnin Turin ranar 25 ga watan Fabrariru.

Rumbun Labarai
Toni Kroos ya soki gasar ƙwallo ta Saudiyya game da raina tasirin Ronaldo
Victor Osimhen ya ci ƙwallo ta 200 a rayuwarsa ta wasa
Atletico Madrid ta ce ta cim ma yarjejeniya da Atalanta kan ɗanwasan gaban Nijeriya Ademola Lookman
Real Madrid za ta sake karawa da Benfica a wasan cike gurbi na Gasar Zakarun Turai
Mourinho ya bai wa Kocin Real Madrid haƙuri bayan Benfica ta doke Madrid a Gasar Zakarun Turai
CAF ta dakatar da kocin Senegal da Achraf Hakimi
Cole Palmer na son komawa Man United, Liverpool ba za ta rabu da kyaftin dinta, Virgil van Dijk ba
'Yanwasan Senegal sun samu kyautar kuɗi da fuloti saboda lashe Kofin AFCON
Dubban mutane sun halarci bikin karrama Zakarun Kofin AFCON a Senegal
Real Madrid ta sallami Xabi Alonso, ta nada Alvaro Arbeloa sabon koci
Hukumar CAF ta yi tir da rashin ɗa'a a zagayen kwata-fainal na AFCON 2025
Ɗan wasan Ghana Semenyo ya koma Man City daga Bournemouth kan dala miliyan 87
Yadda ƙarin kuɗaɗen tallafi ke taimaka wa mata ‘yanwasan ƙwallon ƙafa da ke fama da nakasa a Kenya
Wane ne Liam Rosenior, sabon kocin Chelsea?
Manchester United ta kori kocinta Ruben Amorim bayan ya soki shugabancin kungiyar
An sallami Anthony Joshua daga asibiti
Abubuwa 5 game da mai jiran Man United ta ci wasa 5 a jere, wanda ya kwana 452 ba aski
Yadda Tanzania ta tsallaka gaba da maki biyu kacal a gasar AFCON 2025
Hatsarin mota ya rutsa da Anthony Joshua a jihar Ogun ta Nijeriya
AFCON 2025: Za a fara wasannin ƙarshe na matakin rukuni don tantance ƙasashe 16 masu tsallakawa gaba