Gwamnatin Kebbi ta bayar da umarnin rufe duka makarantun gwamnati da na kuɗi a jihar

Wannan na zuwa ne bayan sace ɗalibai mata 25 daga wata makaranta da ke Maga.

By
Makarantar da kawai ba ta cikin jerin waɗanda aka rufe ita ce Kwalejin Kiwon Lafiya da Ungozoma da ke Birnin Kebbi, babban birnin jihar.

Gwamnatin Jihar Kebbi ta umarci rufe dukkan makarantun sakandare na gwamnati da na kuɗi tare da dukkan manyan makarantun gaba da sakandare a faɗin jihar.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da Kwamishinan Ilimi na Gaba da Sakandare Alhaji Issa Abubakar-Tunga da Kwamishinar Ilimi ta Firamare da Sakandare, Dakta Halima Bande, a Birnin Kebbi.

Kwamishinonin sun bayyana cewa rufe makarantun gwamnati da na kuɗi a jiha ya zama dole sakamakon hare-haren da aka kai a wasu sassan jihar kwanan nan.

Sun lissafa makarantun gaba da sakandare da abin ya shafa kamar haka:
Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi da ke Dakingari da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Abdullahi Fodio da ke Aliero da Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Jega da Kwalejin Ilimi ta Adamu Augie da ke Argungu da Makarantar Sharar Fagen Shiga Jami’a ta Yauri.

Sai dai sun ce makarantar da kawai ba ta cikin jerin waɗanda aka rufe ita ce Kwalejin Kiwon Lafiya da Ungozoma da ke Birnin Kebbi, babban birnin jihar.

Yayin da suke kira ga dukkan shugabannin makarantun da su bi umarnin gwamnati, kwamishinonin sun shawarce su da su kasance cikin natsuwa domin za a sanar da sabuwar ranar koma makarantun nan gaba.

Wannan na faruwa ne bayan sace dalibai mata 25 daga wata makaranta da ke Maga.