Haɗakar al'adu: Girke-girken abincin Turkiyya da Nijeriya masu kamanceceniya
Makarantar girke-girken abincin Turkiyya ta bazara ta Cibiyar Yunus Emre ta haɗa masu dafa abinci daga sassan duniya don musayar dabaru da al'adu da kuma dandano daga Anatolia zuwa Afirka.
Cibiyar Yunus Emre (YEE) ta sake buɗe ƙofofinta ga ƙwararrun masu dafa abinci na duniya. A wannan shekarar, masu dafa abinci daga ƙasashe 13 daga sassan duniya ne suka samu halartar "Makarantar Abincin Turkiyya ta bazara," wani ɓangare na shirye-shiryen bazara na YEE wanda ya karɓi ɗalibai 735 daga ƙasashe 69.
Tsawon makonni, mahalarta sun samu damar ganin ire-iren girkin al'adun Turkiyya daban-daban, inda suka ziyarci birane kamar Istanbul, da Konya, da Gaziantep, da Şanlıurfa don ganin yadda ake sarrafa abincin al’adun ƙasar da kai tsaye.
Masu girke-girken sun yi aiki tare da ƙwararrun masu hada girkin Turkiyya, inda suka koyi dabarun girke-girken gargajiya na ƙasar da kuma fasahar daidaita ɗanɗano.
Baya ga girke-girke, hamalarta shirin sun samu damar ganin yadda iyalai ‘yan Turkiyya ke cimaka, kan sun ziyarci wararen tarihi da al’adu, sannan sun samu ƙarin fahimta kan tarihin abincin da suka girka.
A birnin Istanbul, tawagar mahalarta shirin sun kai ziyara wurin girke-girken fadar Ottoman, tare da ɗanɗana asalin shayin kofi na Turkiyya, sannan sun haɗu da ƙwararren mai yin alawar baklava wato Nadir Güllü wanda ya nuna musu fasahar yin baklava mai kyau.
Mahalartan sun nuna sha'awar nuna ƙwarewar da dabaru da kuma ɗanɗanon abincin Turkiyya da suka koya zuwa ƙasashensu.
Mafi yawa daga cikinsu sun nuna jin daɗinsu na gano irin sinadaren haɗa abincin Ottoman da na Anatoliya, yayin da wasu kuma suka samu ƙwarin gwiwa da yadda aka hada kayayyaki da kuma sinadaran cikin gida wajen girka abincin na gargajiya.
Ƙirƙira da haɗa ire-iren abinci
Daga cikin mahalarta shirin, 'yar Nijeriya Maryam Ahmed ta zama zakarar gwajin dafi a koƙarin da ta yi wajen haɗa girke-girken da ta koya a Turkiyya da na girki na al'adun ƙasarta.
A matsayinta na matashiyar 'yar kasuwa, ta sanya wannan ilimin da ta koya a wurin sana’arta ta siyar da abinci mai suna ‘‘Aure’’ inda take haɗa ɗanɗanon Turkiyya da na arewacin Nijeriya.
A kantin nata, akan girka abincin al’adun Turkiyya da na Arewacin Nijeriya, waɗanda galibi manyan kafofin watsa labarai ba su cika mayar da hankali a kansu ba duk da cewa ana yin su a bukukuwan ala’ada, ga su launuka masu kyau da dauƙar hankali ga kuma al'adun ciye-ciye na abinci daban-daban.
Ire-iren abinci a kantin na Aure ya nuna haɗakar abincin Turkiyya da na Arewacin Nijeriya, wanda aka tsara shi da kyau kuma ciki hikima don haɗa al'adun ƙasashen biyu.
Baya ga abincin gargajiya na Turkiyya kamar pide, kebabs, da Ali Nazik, baƙi ko masu saye za su iya jin daɗin cin miyar ganye da miyar kuɓewa da kuma naman rago, ga kuma uwa-uba abincin Arewacin Nijeriya kamar masa da ɗanɗeru, tare da shinkafa irin ta Turkiyya da farantin mezze.
Ko wane abinci na da haɗin ɗanɗanon Anatolian da kayan ƙanshi na gida na Nijeriya da inda suke samar da sabon dandano kana masu kamanceceniya.
Maryam Ahmed ta ce burinta shine ta gabatar da wata tsiga ta daban da ake kallon Arewacin Nijeriya, yankin da galibi ake nuna labaran rikice-rikice da matsin tattalin arziki da kuma rashin kwanciyar hankali.
Ta hanyar girkinta, tana da burin haskaka al'adunta masu ƙyau, da annashuwa, da kuma zurfafan al'adun al’umma cike da tarba da karamci.
Bayan tafiye-tafiyen da ta yi a garuruwan ƙauyuka don koyon girke-girken gargajiya, yanzu haka tana koƙarin haɗa waɗannan ainihin ɗanɗanon Arewacin Nijeriya da na Turkiyya, don nuna ƙyawu da kuma juriyar al’ummarta ta hanyar abinci.
Baya ga abinci, kantin Aure yana samar da yanayin cimakar tare wanda ya samo asali daga zamantakewar iyali, da labarai, da bukukuwa, kamanceceniyar dabi'un al'ummomin Turkiyya da na Arewancin Nijeriya.
Ta wannan kamanceceniyar al’adu, Maryam tana da burin gabatar da ɗanɗanon Anatolian ga ‘yan Nijeriya yayin da take nuna wadatar kayayyaki da sinadaren abinci na Arewacin Nijeriya.
Ta hanyar shirye-shirye kamar na Makarantar Abincin Turkiyya ta bazara da kuma na kantin abinci na Aure na Maryam Ahmed, ɗanɗanon abincin al’adu na Turkiyya zai ci gaba da samun ƙarin mutane a duniya da ke son girke-girken yankin, tare da haɓaka musayar al'adu, da fahimtar juna, da kuma jin daɗin cin abinci tare.
Haɓaka Al'adun Turkiyya a Duniya
Tun bayan buɗe ofishinta na farko a ƙasashen waje a shekarar 2009, Cibiyar Yunus Emre ta bunƙasa zuwa wata cibiya ta duniya inda take da ofisoshi 92 a ƙasashe 68, kana tana haɗa mutane da Turkiyya da kuma haɓaka harshe, da fasaha, da kuma al'adunta.
Tare da mai da hankali kan haɓaka tattaunawa, da fahimtar juna, da kuma musayar al'adu, cibiyar tana shirya shirye-shirye tun daga darussan iya harshe da baje-koli da kuma shirye-shiryen kara ilimi.
Ayyukanta a faɗin Afirka da sauran yankunan ba wai kawai suna gabatar da al'adun Turkiyya ga ƙarin wasu mutane ba ne, har da ƙarfafa dangantaka ta tsawon lokaci da kuma wayar da kai kan al'adu tsakanin Tukiyya da al'ummomi a duk faɗin duniya.