| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
1 minti karatu
Iran ta sha alwashin gwabza yaƙi da duk ƙasar da ta yi gangancin kai wa Khamenei hari
Shugaba Pezeshkian ya yi gargaɗin ne bayan Trump ya yi barazanar kai hari kan shugaban addini na Iran, a yayin da aka gudanar zanga-zanga kan matsin tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar.
Iran ta sha alwashin gwabza yaƙi da duk ƙasar da ta yi gangancin kai wa Khamenei hari
Ya yi wannan gargaɗi ne bayan shugaban Amurka Donald Trump a wata hira da ya yi da Politico, ya bayyana Khamenei a matsayin “mutum mara lafiya,” / AP
19 Janairu 2026

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ranar Lahadi ya yi gargaɗin cewa za su gwabza yaƙi da duk ƙasar da ta kuskura ta kai hari kan Shugaban Addini na ƙasar Ali Khamenei, a yayin da ake ci gaba da musayar yawu tsakanin Tehran da Washington kan zanga-zangar da ake yi a Iran.

“Duk wani hari da za a kai wa babban shugaban ƙasarmu yana nufin ƙaddamar da gagarumin yaƙi kan ƙasar Iran,” in ji Pezeshkian a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa X.

Masu AlakaTRT Afrika - An buɗe sararin samaniyar Iran bayan rufe shi na wucin-gadi

Pezeshkian ya ɗora alhakin taɓarɓarewar tattalin arzikin Iran kan abin da ya bayyana a matsayin shekaru aru-aru da Amurka da ƙawayenta suka kwashe suna ƙaƙaba wa ƙasarsa takunkumai lamarin da ya jefa ‘yan ƙasar cikin matsanancin hali.

“Ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka jefa al’ummar Iran cikin mawuyacin hali shi ne ƙiyayya da tsantsar rashin imani na gwamnatin Amurka wadda ta lafta mana takunkumai,” in ji shi.

Ya yi wannan gargaɗi ne bayan shugaban Amurka Donald Trump a wata hira da ya yi da Politico, ya bayyana Khamenei a matsayin “mutum mara lafiya,” sannan ya ce Iran “ƙasa ce mafi muni da ake rayuwa,” inda ya ƙara da cewa ƙasar tana buƙatar sabbin shugabanni.

Rumbun Labarai
Iran ba za ta amince da bukatu barkatai ba - Shugaba Pezeshkian
Trump ya yi barazanar ɗaukar 'mataki mai tsanani' kan Iran yayin da Netanyahu ya tafi Washington
Fidan na Turkiyya ya ce amfani da hare-haren sama ba zai rushe gwamnatin Iran ba
Shugaban Iran Pezeshkian ya bayyana tattaunawar nukiliya da Amurka a matsayin 'ci gaba' ga Tehran
Turkiyya da Saudiyya sun jaddada goyon bayansu ga haɗin kan Somaliya da zaman lafiyar yankin
Khamenei ya yi gargaɗi kan yaƙin yanki idan Amurka ta kai hari kan Iran
Iran ta ayyana rundunonin sojin ƙasashen Turai a matsayin 'ƙungiyoyin ta'addanci'
A 'shirye' Iran take don 'yarjejeniyar nukiliya ta gaskiya da adalci': Ministan Harkokin Wajen Iran
Waɗanne abubuwa ne za su iya faruwa idan Amurka ta kai hari Iran?
Iran ta ce duk maƙociyar da ta bari aka yi amfani da ita wurin kai mata hari 'abokiyar gaba' ce
Isra'ila na karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon, ta ci gaba da kai hari
Manyan jami'an China sun tattauna da Ƙungiyar OIC a yanayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ƙara muni
Yaƙin da ake yi da ta'addancin Daesh yana ƙara ƙarfi: Erdogan
Iran ta gargaɗi Amurka: 'Za mu ɗauki kowane irin hari a matsayin cikakken yaƙi a kanmu'
Turkiyya ba ta goyon bayan tsoma bakin ƙasashe waje a kan Iran – Erdogan
Adadin mutanen da suka mutu a zanga-zangar Iran ya kai  4,000: Rahoto
Syria ta cim ma tsagaita wuta don karɓe iko da arewa maso gabas daga hannun ‘yan ta’addan YPG
Syria ta ayyana harshen Kurdanci a matsayin 'harshen ƙasa', sannan ta ba Kurdawa haƙƙin 'yan ƙasa
An buɗe sararin samaniyar Iran bayan rufe shi na wucin-gadi
Trump ya yi barazanar ‘ɗaukar tsattsauran mataki’ idan Iran ta rataye masu zanga-zanga