Iran ta harba makamai masu linzami kan sansanin sojin Amurka da ke Jordan, sannan ta yi iƙirarin kai hari kan wasu jiragen yaƙin Amurka biyu a matakin ramuwar gayya ga hare-haren da Amurka ta kai mata kwanan nan.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Tehran ke faɗaɗa hare-haren da take kai wa kadarorin Amurka da jiragen ruwa na dakon mai a yankin.
Rundunar sojin sama ta Jordan ta ce ta kakkaɓo makamai masu linzami 18 daga cikin 20 da Iran ta harba kan sansanin sojin Amurka da ke ƙasar.
Kazalika wani mai magana da yawun rundunar sojin ƙasar ya ce, sauran makamai masu linzamin biyu sun sauka a wuraren da babu jama’a kuma ba su yi sanadiyyar mutuwar fararen-hula ba ko kuma lalata wasu kayayyakin more rayuwa ba.
Wannan matakin ya biyo bayan sanarwar da rundunar kare juyin juya hali ta Iran (IRGC) ta fitar, inda ta yi iƙirarin kai hari kan sansanin sojin Amurka da ke Jordan da kuma jiragen yaƙin Amurka ƙirar DDG-119 da DDG-53, waɗanda ke ɗauke da makamai masu linzami a jiragen ruwa da kuma fasahar tsarin yaƙi ta Aegis.
A wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya fitar, IRGC ta yi iƙirarin cewa ta mayar da martani mai ƙarfi kan "ayyukan zalunci da mugunta da aka yi kan tankokin mai na Iran da kuma jiragen ruwanta," tana mai cewa ta yi ɓarna mai yawa ga jiragen ruwan da aka turo da kuma cibiyoyin Amurka.
Barazana ga tashar jiragen ruwa
Hare-haren makamai masu linzami tsakanin ƙasashen biyu suna faruwa ne a daidai lokacin da tashin hankali da kuma faɗa tsakanin jiragen ruwansu a Tekun Gulf ke ta'azzara.
Rundunar sojin ruwan Iran ta yi gargaɗin cewa za ta kai harin ramuwar gayya kan tankunan mai da ke tashoshin jiragen ruwan Kuwait da Bahrain, inda ta yi kira ga ma'aikatan jiragen da su fice nan-take bayan rahotannin hare-haren da Amurka ta kai wa jiragen ruwan Iran, in ji kamfanin dillancin labarai na IRIB.
A wata sanarwa a hukumance da IRIB ta fitar, hukumomin ruwan sun sanar da cewa an yi gargaɗi a matsayin martani na kai-tsaye ga hare-haren sojojin Amurka da ke kai wa jiragen ruwan Iran da dama hari.
Rundunar sojojin ruwan ta yi kira ga dukkan ma'aikatan jiragen ruwa da ke makale a tashoshin jiragen ruwa a Kuwait da Bahrain da su bar jiragen ruwansu ba tare da ɓata lokaci ba, tana mai gargaɗin cewa jiragen ruwan suna daga cikin abubuwan da sojoji za su kai musu hari.
Gargaɗin ya biyo bayan wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Tasnim na Iran ya fitar a ranar Talata da ta wuce, inda ya ce wani makami mai linzami na Amurka ya afka kan wani jirgin ruwan mai na Iran daga wani wuri mai nisan kilomita 7.4 daga Tsibirin Kharg a Tekun Gulf.
Tasnim ya ruwaito cewa makamin ya afka jirgin da ke kusa da yankin tsibirin da ke da tashar jiragen ruwa.
Ba a samu wani rahoto na asarar rai ba, kuma an yi nasarar kwashe ma'aikatan jirgin baki ɗaya.
Daga baya kafar IRIB ta ruwaito cewa sojojin Amurka sun kai hari kan wani jirgin ruwan mai na Iran na biyu da ke bakin tekun Jask a kudancin Iran, a wajen Tekun Gulf.





















