Gwamnatin Ghana ta sanar da nasarar ceto tare da dawo da ‘yan kasarta 28 daga Côte d’Ivoire bayan sun fada hannun wata babbar kungiyar safarar mutane da ta yi musu alkawarin kai su Turai.
A cikin wata sanarwa da Ministan Harkokin Wajen Ghana ya wallafa a shafinsa na X ranar 10 ga watan Mayu, hukumomi sun bayyana cewa yawancin wadanda aka ceto matasa ne, kuma an dawo da su Ghana bayan wani aikin haɗaka da jami’an tsaro tare da ma’aikatan ofishin jakadancin Ghana da ke Abidjan suka gudanar.
Sanarwar ta ce wadanda aka ceto yanzu suna cikin koshin lafiya a Ghana, kuma suna taimaka wa hukumomi wajen ci gaba da bincike kan kungiyar safarar mutanen.
Ministan harkokin wajen Ghana, Samuel Okudzeto Ablakwa ya bayyana cewa masu safarar sun karbi makudan kudade daga hannun wadanda abin ya shafa tare da yi musu alkawarin “rayuwa mai dadi a Turai.”
“Mun yi nasarar ceto tare da dawo da ‘yan Ghana 28 daga Côte d’Ivoire wadanda suka fada hannun wata kungiyar safarar mutane mai matukar kwarewa,” in ji ministan.
Ya kara da cewa, “An yaudari mutanen da alkawarin rayuwa mai kyau a Turai bayan an kwace makudan kudade daga hannunsu. Abin farin ciki, yanzu sun dawo Ghana cikin koshin lafiya bayan wannan aiki na musamman da muka gudanar.”
Ministan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin Shugaba John Dramani Mahama ba za ta yi watsi da duk wani dan Ghana da ke cikin matsala a wata kasa ba.
“Gwamnatin Mahama ba za ta taba barin wani dan Ghana cikin hali na ƙunci ba,” in ji shi.
Gwamnatin Ghana ta kuma yaba wa hukumomin Côte d’Ivoire bisa hadin kai da musayar bayanan sirri da suka taimaka wajen samun nasarar aikin.
A halin yanzu, hukumomi sun gargadi matasa da su kasance masu taka-tsantsan domin kauce wa fadawa tarkon kungiyoyin safarar mutane da hukumomin daukar aiki na bogi da ke yaudarar mutane da alkawarin ayyukan yi da tafiya kasashen waje.
Ma’aikatar ta bukaci jama’a da su tabbatar da sahihancin duk wata tayin aiki ko tafiya ta hanyar tuntubar hukumomin gwamnati da ofisoshin jakadancin Ghana kafin daukar mataki.
Hukumomi sun ce ana ci gaba da kokarin rusa kungiyar masu safarar mutanen tare da gurfanar da wadanda ke da hannu a lamarin a gaban kuliya.













