| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
'Yansandan Nijeriya sun kama likitoci kan zargin safarar mutane da cire musu ƙoda
Daga cikin waɗanda aka kama akwai Dakta Benjamin Oyime wanda likitan ƙoda ne a asibitin Wellington da ke unguwar Life Camp a Abuja, kamar yadda rundunar 'yansandan Nijeriya ta tabbatar.
'Yansandan Nijeriya sun kama likitoci kan zargin safarar mutane da cire musu ƙoda
’Yansandan sun ce waɗanda ake zargin sun yi amfani da matsalolin kuɗi da mutanen ke fuskanta wajen yardarsu domin cire musu sassan jiki ba bisa ƙa’ida

Rundunar ’Yansandan Nijeriya ta kama wasu mutane huɗu da ake zargi da hannu a cikin wata ƙungiyar masu safarar mutane da cire sassan jikin bil’adama, wadda ake zargin tana gudanar da ayyukanta a Jihar Nasarawa.

Waɗanda ake zargin su ne Emmanuel Ode, mai shekaru 23 da Dakta Benjamin Oyime, mai shekaru 48, likitan ƙoda kuma likita a asibitin Wellington da ke Life Camp, Abuja.

Haka kuma akwai Dakta Daniel Otukpa, mai shekaru 53, shi ma likitan ƙoda ne kuma Mukaddashin Daraktan Ayyukan Kula da Lafiya na Asibitin Wellington da kuma David Idoko, mai shekaru 25.

Jami’an rundunar Special Tactical Squad ne suka kama su a yayin wani samame na musamman a ranar 19 ga watan Agustan 2026, a Auta Balifi da ke Ƙaramar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yansandan, CSP Ani Iniedu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

A cewar Iniedu, Ode ya amsa cewa yana da hannu wajen ɗaukar waɗanda abin ya shafa ta hanyar yaudararsu.

“A ranar 24 ga Afrilun 2026 ya bayyana cewa ya yaudari wani Samuel Ezekiel, mai shekaru 22, zuwa Wellington Hospital da ke Life Camp, Abuja, inda ake zargin an cire masa ƙodarsa a kan kuɗin dala 1,250 na Amurka, wanda ya yi daidai da Naira 1,700,000 bisa farashin musayar kuɗi na yanzu.

“Wani mutum na biyu da abin ya shafa ya ce shi dai wannan mutumin ne ya yaudare shi a shekarar 2022 zuwa wani asibiti, inda aka cire masa ƙoda, sannan aka biya shi Naira miliyan 7,” in ji sanarwar.

’Yansandan sun ce waɗanda ake zargin sun yi amfani da matsalolin kuɗi da mutanen ke fuskanta wajen yardarsu domin cire musu sassan jiki ba bisa ƙa’ida ba.

“Bincike ya gano cewa waɗanda ake zargin da abokan aikinsu sun mayar da hankali ne kan matasa masu rauni da waɗanda ba su da ilimi a Jihar Nasarawa da kewayenta, inda suka yi amfani da matsananciyar buƙatar kuɗi da suke ciki wajen yardarsu domin cire musu sassan jiki ba bisa ƙa’ida ba.

“Shaidun da aka tattara sun nuna cewa waɗanda ake zargin sun ƙirƙiri takardun hukuma na bogi, ciki har da sunayen waɗanda abin ya shafa, Lambobin Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN), takardun haihuwa, takardun bayyana shekaru, takardun rantsuwa na kotu da takardun amincewa, domin sauƙaƙa gudanar da waɗannan ayyukan laifi.”

’Yan sandan sun ce an kuma ƙwato wasu tufafi da ake zargin an saya da kuɗin da aka samu daga aikata laifin, waɗanda aka gabatar a matsayin shaidu yayin samamen.

Rundunar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin cafke wasu mutane da ake zargin suna da alaƙa da wannan ƙungiyar.