| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Matatar Dangote ta koma sayar da fetur a naira, ta ƙara farashin lita da N140
Wannan na zuwa ne mako guda bayan matatar man ta Dangote ta dakatar da loda fetur ga manyan motoci tare da sauya tsarin biyan kuɗi zuwa dalar Amurka, matakin da ya jefa kasuwar man fetur cikin ruɗani.
Matatar Dangote ta koma sayar da fetur a naira, ta ƙara farashin lita da N140
An sanar da komawa amfani da naira ne a cikin wata sanarwa da sashen kasuwanci na matatar ya aika wa ‘yankasuwar man fetur a ranar Laraba,

Matatar Mai ta Dangote ta jingine matakin da ta ɗauka a kwanakin baya na sayar da fetur da dalar Amurka inda ta koma sayar da shi da naira. Sai dai kuma ta ƙara farashin N140 kan kowace lita da take sayar wa dillalai.

Wannan na zuwa ne mako guda bayan matatar man ta Dangote mai ƙarfin tace ganga 650,000 a rana ta dakatar da loda fetur ga manyan motoci tare da sauya tsarin biyan kuɗi zuwa dalar Amurka, matakin da ya jefa kasuwar man fetur cikin ruɗani, ya takaita samar da fetur, sannan ya haddasa tashin farashi a defo-defo.

An sanar da komawa amfani da naira ne a cikin wata sanarwa da sashen kasuwanci na matatar ya aika wa masu kasuwar man fetur a ranar Laraba, kuma dandalin masana'antar mai na Petroleumprice.ng ya tabbatar da hakan.

Masu AlakaTRT Afrika - Matatar Dangote ta koma amfani da farashin dala don sayar da manta maimakon naira

Sanarwar ta nuna cewa farashin fetur a wurin lodin matatar ya tashi daga N1,075 kan lita zuwa N1,215 kan lita, wanda ke nuna ƙarin N140, ko kuma kashi 13.02 cikin 100. Haka kuma, farashin lodin jiragen ruwa ya tashi daga N1,441,575 kan kowane metric tonne zuwa N1,602,495 kan kowane metric tonne.

Wannan mataki ya kuma sa masu zaman kansu da ke sayar da man fetur suka dakatar da lodin fetur daga matatar, inda suka ce ba su da damar samun isasshen kuɗin waje da ake buƙata domin gudanar da cinikin.

Masu ruwa da tsaki a masana'antar sun yi gargadin cewa wannan tsari zai ƙara buƙatar kuɗaɗen waje, ya karya darajar naira, sannan ya haifar da ƙarin farashin fetur a faɗin ƙasar.

Bisa kiyasin cewa Nijeriya na amfani da kusan lita miliyan 50 na fetur a kullum, ana hasashen masu kasuwar man fetur za su buƙaci kusan dala miliyan 40 a kowace rana, wato fiye da dala biliyan 14 a shekara, domin ci gaba da sayen fetur daga matatar idan aka ci gaba da tsarin biyan kuɗi da dalar Amurka.

Matatar Dangote ta kare matakin da ta ɗauka na wucin-gadi na karɓar dalar Amurka, tana mai cewa ta daina samun isasshen ɗanyen mai a ƙarƙashin shirin gwamnatin tarayya na naira na ɗanyen mai, wanda ya tilasta mata sayen ƙarin ɗanyen mai daga kasuwannin duniya ta hanyar amfani da dalar Amurka.