| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Har yanzu Amurka ba ta ba da bizar gasar Kofin Duniya ga tawagar ƙwallon ƙafar ƙasarmu ba: Iran
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Iran ta ce kawo yanzu Amurka ba ta bai wa tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar biza ba domin halartar gasar cin kofin duniya ta 2026 a ƙasar, yayin da Tehran ke kira ga FIFA ta tabbatar da damar shiga ga duk tawogogin gasar.
Har yanzu Amurka ba ta ba da bizar gasar Kofin Duniya ga tawagar ƙwallon ƙafar ƙasarmu ba: Iran
Magoya bayan a Tehran a wani bikin bankwana ga tawagar ƙwallon ƙafa ta Iran a gabannin tafiyarsu gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 / Reuters

Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Iran ya ce ba a bayar da biza ga tawagar ƙwallon ƙafar ƙasarsa domin shiga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 a Amurka ba, kamar yadda kafar watsa labaran gwamnatin ƙasar ta ruwaito.

"Gobe ko jibi za mu yi wata muhimmiyar ganawa da hukumar FIFA. Dole su ba mu tabbaci, saboda har yanzu ba a warware batun bizar ba," kamar yadda kamfanin dillancin labarai mallakin gwamnatin ƙasar IRNA ya ambato shugaban hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar Mehdi Taj yana cewa ranar Alhamis.

"Ba mu samu ko wane labari ba daga ɗaya ɓangaren game da wanda aka bai wa biza. Babu bizar da aka bayar kawo yanzu," kamar yadda ya ƙara bayyanawa.

Taj ya ce ana tsammanin ‘yanwasan za su tafi babban birnin Turkiyya Ankara domin ɗaukar hoton yatsunsu a wani ɓangare na aikin ba da bizar.

"Dole ‘yanwasan su tafi Ankara domin ɗaukar hoton yatsunsu, amma muna ƙoƙarin shirin yin wannan a Antalya domin kada a samu buƙatar tafiya Ankara," a cewarsa.

Iran ta kasance cikin yaƙi da Amurka da Isra’ila tun ranar 28 ga watan Fabrairu, duk da cewa an samar da yarjejeniyar tsagaita wuta tun ranar 8 ga watan Afrilu.

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran ya ce wata "ƙasa mai karɓar baƙunci ba za ta iya amfani da jayayyar siyasa ba ko takunkumi ko kuma matakin ƙashin kanta na cikin gida" ta hana wata tawaga halartar gasar cin kofin duniya ba.

"Idan hukumar da ta shirya gasar ba za ta iya tabbatar da cewa duk tawagogin da suka samu shiga gasar ciki har da Iran, za su iya shiga ƙasa mai masauƙin baƙi ba tare da wariya ko ƙuntatawa ba ... yarda da gasar cin kofin duniyar kanta za ta raunata ," kamar yadda Kazem Gharibabadi ya wallafa a shafinsa na X.

Tehran da Washington ba su da dangantaka ta diflomasiyya tun shekarar 1980 bayan rikicin garkuwa da mutane a ofishin jakadancin Amurka, wanda ya faru bayan juyin juya halin Musulunci na ƙasar da ya hamɓarar da Shah da Amurka ke goya wa baya.

Iran ta yi bikin bankwana ranar Laraba ga tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasar yayin da tawagar ke shirin fafatawa a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 , wadda Amurka da Mezio da Kanada ke karɓar baƙuncinta tare.

Tawagar ƙwallon ƙafar Iran, wadda aka sani da suna Team Melli, za ta kasance a Tucson, a jihar Arizona yayin gasar cin kofin dujiyar.

‘Yan Iran za su fara gasar cin kofin duniya ne da karawa da tawagar New Zealand a Los Angeles ranar 15 ga watan Yuni kafin su shirya domin karawa da Belgium da Masar a rukuni na G.