| Hausa
WASANNI
1 minti karatu
Antonio Conte ya sake zama kocin Italiya
Conte mai shekaru 56, ya taɓa riƙe Italiya a baya, inda ya kai tawagar zuwa wasan dab da na ƙarshe a Gasar Kofin Turai ta Euro 2016.
Antonio Conte ya sake zama kocin Italiya
Antonio Conte ɗan asalin Italiya ne mai shekaru 56 / Reuters

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Italiya, FIGC, ta naɗa Antonio Conte kocin tawagar ƙasar don ceto ta daga rashin tagomashin da ya hana ta zuwa Gasar Kofin Duniya har sau uku a jere.

Italiya ta taɓa cin Kofin Duniya har sau huɗu, amma yanzu ta kwashe shekaru fiye da goma babu tagogmashi, wanda ke nuna tana buƙatar garambawul.

Rahotanni na cewa Conte, wanda zaƙaƙurin koci ne da ya riƙe tawagogi a ciki da wajen Italiya, kamar Juventus, Napoli, Chelsea, zai sanya hannu kan kwantiragin shekaru huɗu.

Hakan zai ba shi damar ƙaddamar da shirin da zai farfaɗo da tagomashin Italiya domin shirya neman cancantar buga gasar Kofin Duniya ta 2030, wadda za a yi a Sifaniya, Portugal, da Maroko.

Mai shekaru 56, Conte ya taɓa riƙe Italiya daga 2014 zuwa 2016, inda ya kai tawagar zuwa wasan dab da na ƙarshe a Gasar Kofin Turai ta Euro 2016.

A baya-bayan nan, Conte wanda ɗan asalin Italiyan ne, ya bar aikin horar da ƙungiyar Napoli ta Italiya, bayan ya ciyo musu kofin Serie A da na Super Cup.