| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Hare-haren Iran sun ragargaza cibiyoyin leken asirin Amurka a Gabas ta Tsakiya: Rahoto
Hare-haren makamai masu linzami da na jiragen sama marasa matuki na Iran sun lalata cibiyoyin leken asiri da tsarin tattara bayanai da kuma kayyayakin sa ido na Amurka a Gabas ta Tsakiya.
Hare-haren Iran sun ragargaza cibiyoyin leken asirin Amurka a Gabas ta Tsakiya: Rahoto
Hare-haren Iran sun haifar da barnar biliyoyin kadarori na hukumar leken asirin Amurka

Hare-haren makamai masu linzami da na jiragen sama marasa matuki na Iran sun mummunar ragargada cibiyoyin leƙen asirin Amurka da kayayyakin aiki da suka kai na biliyoyin daloli a Gabas ta Tsakiya, a cewar rahoton kafar NBC News, tana mai ambaton wasu majiyoyi huɗu da ke da masaniya kan lamarin.

Hare-haren sun lalata gine-gine da tsarin na’urar tattara bayanan sirri da kayayyakin sa ido da hukumar CIA da sauran hukumomin leƙen asirin Amurka ke amfani da su, inda aka bayyana girman ɓarnar da aka yi a matsayin mafi girma da muni fiye da duk wanda hukumar leƙen asirin Amurka ta taba samu.

A cewar majiyoyin, hare-haren sun yi wa wurare da kayayyakin aiki da dama na haɗin gwiwa da hukumomin leƙen asiri da sojojin Amurka suke amfani da su, wanda hakan ya sa Majalisar Dokokin Amurka ta ware kuɗaden gaggawa don sake ginawa da kuma maye gurbinsu.

Hare-hare kan tashoshin CIA da tsarin tattara bayanai

Daga cikin wuraren da aka kai wa hari a lokacin rikicin har da wata tashar CIA da ke Riyadh da wata cibiya a gabashin Iraki da kuma wuraren tattara bayanai da na'urorin leƙen asiri masu mahimmanci da aka baza su a yankin, a cewar jami'an Amurka da na yankin Gulf.

A lokacin farkon fafatawar, Iran ta kai hare-hare kan cibiyoyin tattara bayanai da tsarin tsaron sararin samaniya na Amurka.

Hotunan tauraron dan adam da shaidun gani da do sun nuna yadda aka lalata tsarin na'urori fasahohi, ciki har da na’urar AN/TPY-2 a Jordan da kuma na’urar AN/FPS-12 a Qatar, da kuma wasu wuraren aikin Amurka da aka lalata a faɗin yankin Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain da Kuwait da kuma Saudiyya.

Mummunar barnar ya haifar da tambayoyin gaggawa a cikin rundunar sojojin Amurka da kuma cibiyoyin leƙen asiri na ƙasar game da ikon Washington na kare kadarorinta a faɗin yankin.

Rage yawan tarin kayayyaki

Hare-haren sun kuma haifar da mummunar barna ga tarin kayayyakin tsaron sararin samaniya na Amurka.

Wani rahoto da Cibiyar Nazarin Dabaru da binciken Kasashen Duniya (CSIS) ta wallafa a watan Yuli ya kiyasta cewa tsakanin watan Fabrairu zuwa Yuli, an lalata kusan kashi 65 cikin 100 na na'urorin dakile hare-haren jiragen sama na Amurka, inda na'urorin jirage marasa matuka na THAAD suka ragu da akalla kashi 38 cikin 100.

Rikicin yankin ya ta'azzara sosai bayan da Amurka da Isra'ila suka kaddamar da hare-haren haɗin gwiwa kan Iran a watan Fabrairu, wanda ya sa Tehran ta mayar da martani kan sansanonin soji da cibiyoyin leƙen asiri na Amurka a kasashen da ke karbar bakuncinsu a faɗin Tekun Fasha.

Duk da cewa Iran da Amurka sun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna a tsakiyar watan Yuni, wadda Pakistan ta shiga tsakani, da nufin dakatar da tashin hankali, sai dai aiwatar da yarjejeniyar ya tsaya cak a daidai lokacin da ake ci gaba da takaddama kan sharuɗɗan da kuma hanyar da za a bi mashigar tekun Hormuz.