Ma’aikatar Tsaron Amurka, Pentagon, na shirin janye kimanin sojoji 200 daga Nijeriya, waɗanda aka tura a farkon wannan shekarar domin taimakawa wajen yaƙi da ‘yanta’adda. Hakan zai kawo ƙarshen wani aiki da jami’an Amurka suka ce zai iya zama abin koyi ga ayyukan soji na gaba a nahiyar Afirka.
A daidai lokacin da kimanin sojojin Amurka 50,000 ke yaƙi da Iran, jami’an Amurka da na Nijeriya sun ce ko da yake adadin sojojin da aka tura Nijeriya bai shi da yawa, aikin nasu ya haifar da gagarumin sakamako, ciki har da kashe wani babban shugaban Daesh.
Sai dai kuma, aikin bai samu cikakkiyar nasara ba. Har yanzu ‘yanta’addan ba a gama murƙushe su gaba daya ba, kuma suna ci gaba da kai munanan hare-hare a sassan kasar.
A cikin ‘yan kwanakin nan, ‘yanta’adda sun kashe mutane fiye da 24, ciki har da wani limami, a arewa maso yammacin Nijeriya. Haka kuma, a wani hari da aka kai wani ƙauye a tsakiyar kasar, an kashe akalla mutane 25, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito. A ranar Asabar kuma, ‘yanta’addan sun kai wani gagarumin hari kan wani sansanin sojoji a arewa maso gabashin ƙasar.
An tura sojojin Amurka zuwa arewa maso gabashin Nijeriya a watan Fabrairu, makonni bayan da Shugaba Donald Trump ya soki Nijeriya kan abin da ya bayyana a matsayin gazawar ƙasar wajen kare Kiristoci daga hare-haren ‘yanta’adda. Sai dai kuma, duka Kiristoci da Musulmi sun kasance cikin wadanda rikicin ya rutsa da su.
Tura sojojin ya ƙara ƙarfafa wata ƙaramar tawagar sojojin Amurka da ke taimaka wa sojojin Nijeriya wajen gano wuraren da ‘yanta’adda suke domin kai hare-hare, ta hanyar amfani da bayanan sirri na Amurka da Nijeriya.
Aikin ya kai kololuwa a watan Mayu, lokacin da rundunar musamman ta Amurka da Nijeriya ta kai wani samame, wanda ya hada da wasu mambobin SEAL Team 6 na rundunar sojin ruwa ta Amurka, inda suka kashe Abu Bilal al-Minuki, wanda ake ganin shi ne shugaban ayyukan Daesh na duniya a zahiri.
Cikin makwanni bayan haka, jami’an sojin Amurka sun ce an kashe wasu ‘yanta’adda fiye da 200 a jerin hare-haren sama da samamen ƙasa, wadanda suka hada da amfani da jiragen yaƙi marasa matuƙa na MQ-9 Reaper na rundunar Special Operations da kuma jiragen AC-130 masu manyan bindigogi.
Mutuwar Al-Minuki da kuma raunana hanyar sadarwar Daesh a Nijeriya su ne manyan alamomin hadin gwiwar da ke ƙara ƙarfi tsakanin rundunonin sojin ƙasashen biyu.





















