| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Mutane sama da 100 sun mutu, da yawa sun ɓata a mummunar ambaliyar da ta addabi Sumatra, Indonesia
Ba a iya zuwa yankuna da dama yayin da hukumomi suke fargabar adadin waɗanda suka mutu zai iya ƙaruwa.
Mutane sama da 100 sun mutu, da yawa sun ɓata a mummunar ambaliyar da ta addabi Sumatra, Indonesia
Yara suna zaune a cikin kwantena na roba yayin da mazauna ke kwashewa ta cikin ruwan ambaliya bayan ruwan sama mai yawa ya sauka a Deli Serdang, Arewacin Sumatra, a ranar 28 ga Nuwamba 2025. / Reuters
29 Nuwamba 2025

Ambaliyar ruwa mai tsanani da zaftarewar ƙasa a tsibirin Sumatra na Indonesia sun kashe aƙalla mutane 116 kuma mutane 42 suna ɓace, in ji Hukumar Kula da Bala'o'i ta Ƙasa (BNPB) a ranar Juma'a.

Shugaban hukumar ta BNPB, Suharyanto, ya ce Arewacin Sumatra shi ne lardin da lamarin ya fi yin ƙamari. Yayin da aka shiga rana ta huɗu a wajen kai martanin gaggawa ta huɗu, aikin ceto na ci gaba da samun cikas saboda wahalar shiga wajen, da lalacewar hanyoyin shiga wajen, da mummunan yanayi.

“A yau, mun samu adadin mutane 116 da suka mutu, har yanzu ba a san inda mutane 42 suke ba,” in ji Suharyanto a taron manema labarai da aka watsa kai-tsaye a tashar YouTube ta BNPB, kamar yadda Jakarta Globe ta rawaito, wadda ta kuma ta bayyana cewa dubban mutane sun rasa gidajensu saboda mummunan yanayi.

Har yanzu ba a iya zuwa yawancin wuraren da abin ya shafa, kuma hukumomi na fargabar cewa adadin mutanen da suka mutu zai iya ƙaruwa.

“Akwai wurare da ba mu iya zuwa ba, inda alamu ke nuna cewa adadin wadanda suka rasa abin ya shafa zai iya karuwa,” kamar yadda ya yi gargadi.

Tawagogin laluben mutanen da lamarin ya shafa na aiki a ƙasa da sama, duk da kasancewa mummunan yanayin da ake ciki yana hana kai manyan injina.

Ana ci gaba da tattaunawa da hukumomin yankin don ba da sabbin bayanai game da asarar rayuka da kuma samar da mahimman kayan aiki da ake buƙata.

Hukumomi sun yi kira ga gwamnatocin yankuna da su gaggauta kafawa cibiyoyin lafiya da dakunan girki na jama'a a wuraren da mutane suka fi yawa.

Rumbun Labarai
Matar shugaban Turkiyya ta gana da shugaban UNRWA kan shirin buɗe ofis a Ankara
Sanatocin Republican 5 sun bi sahun 'yan Democrat don neman sake duba ikon yaki na Trump a Venezuela
An kashe ɗansanda a kusa da Tehran yayin da zanga-zanga kan matsin rayuwa ta mamaye ƙasar Iran
Erdogan da Anwar na son ƙarfafa alaƙar Turkiyya da Malaysia tare da fifita fannin tsaro
Trump ya sanya hannu kan takardar neman cire Amurka daga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da na MDD
Shugaban Rundunar Sojin Iran ya yi barazanar mayar da martani ga Trump da Netanyahu
Abin da ya sa ya kamata Afirka ta damu kan samamen da Amurka ta kai Venezuela
An sayar da kifi mai nauyin kilogiram 240 a kan Naira biliyan 4.5 ($3.2m) a Japan
Me zai faru ga takunkuman da Amurka ta sanya wa Venezuela bayan ta ɗauke Maduro
Tarayyar Afirka ta nuna 'damuwa', Afirka ta Kudu ta nemi a yi taron MDD da gaggawa kan Venezuela
Trump ya gargaɗi Colombia, ya nufi Cuba bayan ya kama Maduro
Amurka ba za ta bari kowa ya ci gaba daga inda Maduro ya tsaya ba - Trump
Martanin duniya na karuwa kan hare-haren da Amurka ta kai wa Venezuela
An fitar da Shugaba Maduro da matarsa daga Venezuela, in ji Trump
Ƙarar bamabamai ta rikita birnin Caracas bayan Trump ya sha alwashin kai hari a ƙasar Venezuela
Zanga-zangar Iran kan matsin tattalin arziki ta rikiɗe zuwa tashin hankali
Hotuna: Wasan tartsatsin wuta da sauran bukukuwa na maraba da Sabuwar Shekara ta 2026
Fiye da mutum 3,000 ne suka mutu a tafiya ci-rani Turai ta Spain a 2025: Rahoto
Somalia ta yi watsi da amincewar da Isra'ila ta yi wa Somaliland a matsayin barazana ga yankin
Turkiyya ta yi tir da Israila kan amincewa da Somaliland