Gobara a wasu gidajen mai ta ƙone Keke Napep 17 da tankokin dakon mai biyu a Kano

Jami'in Hulɗa da Jama'a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.

By
Jami'in Hulɗa da Jama'a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.

Aƙalla babur mai ƙafa uku na Keke Napep 17 tare da tankokin dakon mai biyu ne suka ƙone sakamakon wata gobara da ta tashi a wani gidan mai a Jihar Kano ranar Talata.

Jami'in Hulɗa da Jama'a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.

Abdullahi ya ce lamarin na farko ya faru ne a gidan mai na AA Ayagi, da ke ƙauyen Kanye, a kan titin Gwarzo a karamar hukumar Kabo ta jihar, da misalin ƙarfe 8:45 na dare.

Ya ce, "Mun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 20:45 daga ɗaya daga cikin ma'aikatanmu, Muhammad Wada Abdulsalam, yana bayar da rahoton tashin gobara a gidan mai na AA AYAGI, da ke kan titin Gwarzo."

Jami'anmu daga sashen Rijiyar Zaki sun yi tattaki zuwa wurin da lamarin ya faru, kuma da isowarsu, sun sami wata tankar mai mallakin Kamfanin AA Ayagi, tana ci da wuta yayin da take sauke man fetur.”

Ya ce a lokacin da lamarin ya faru, an riga an sauke mai daga ɓangarori biyu a cikin tankin karkashin kasa, yayin da ake ƙoƙrin sauke ragowar kimanin lita 5,000 na dangogin man, ya kara da cewa gobarar ta lalata motar tankar gaba daya.

Ya ce lamari na biyu ya faru ne a tashar mai ta Al-Wahida Nigeria Limited da ke Rimin Kebe Karshen Kwalta, karamar hukumar Nassarawa, inda wata tankar mai mallakar Kamfanin BA Bello ke ɗauke da kimanin lita 45,000 na dangogin mai ita ma ta kama da wuta.

"Gobarar da ta tashi yayin sauke kayan, ta lalata kan motar tankar da wani ɓangare na jikin tankar, tare da ƙone babur din Keke Napep guda 17 (Adaidaita sahu)," in ji shi.

Ya ce da taimakon Allah ne aka shawo kan gobarar kuma aka hana ta yaɗuwa kuma an samu ceto ragowar man fetur din, da kuma sassan jikin tankar.

A hannu guda kuma wata gobarar ta tashi a Kundila Quarters, kusa da Makarantar SALSA, inda ta lalata ɗaki ɗaya, bandaki ɗaya, da kuma wata hanya a wani ginin gidaje a yankin.

Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jiha, Sani Anas, ya bukaci jama'a, musamman masu gudanar da tashoshin mai da direbobin tankunan mai, da su bi ƙa'idodin kiyaye hatsari yayin sauke mai.