An fitar da Shugaba Maduro da matarsa daga Venezuela, in ji Trump

Shugaban Trump ya sanar da cewa ayyukan sojin Amurka sun samu nasara a ƙasar Venezuela, inda kama Maduro da matarsa yayin wani gagarumin aikin soji.

By
President Trump confirmed that Maduro was removed from power after a US strike. [File photo] / AFP

Shugaba Donald Trump ya sanar a ranar Asabar cewa Amurka ta kai wa Venezuela gagarumin hari, abin da ya haifar da kama Shugaba Nicolas Maduro da matarsa, wadanda aka fitar da su daga ƙasar.

'Amurka ta yi nasarar aiwatar da gagarumin farmaki kan Venezuela da shugabanta, Shugaba Nicolas Maduro, wanda aka kama tare da matarsa aka kuma fitar da su daga ƙasar,' in ji Trump kamar yadda ya faɗa a cikin wata sanarwa da aka wallafa a dandalin sada zumunta Truth Social.

Shugaban na Amurka ya kuma bayyana cewa an gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar hukumomin aiwatar da doka na Amurka.

Wannan labari na ci gaba kuma za a sabunta shi...