Burkina Faso, Mali da Nijar sun yi tir da ɗauke Maduro da Amurka ta yi

Shugabannin Burkina Faso, Mali da Niger sun yi allah wadai da matakin Amurka na kifar da Shugaban Venezuela, Nicolas Maduro, wanda suke da alaƙa mai ƙarfi da shi, inda suka kira matakin a matsayin "cin zarafi."

By
Burkina Faso, Mali da Nijar sun yi Allah wadai da satar Shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro. / Other

Shugabannin Burkina Faso, Mali da Nijar sun yi Allah wadai da yadda Amurka ta tsige shugaban Venezuela, Nicolas Maduro — kasar da suke da kusancin hulɗa da ita — sannan suka bayyana matakin a matsayin “kai hari”.

Kungiyar Kasashen Sahel 'ta yi Allah wadai matuƙa' da tsige Maduro, 'matakin da ya keta dokar ƙasa da ƙasa', in ji wata sanarwa.

Sun yi kira ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi Allah wadai da matakin Amurka, kuma ya yi aiki don dawo da 'doka ta ƙasa da ƙasa' a Venezuela.

Shugaban Burkina Faso, Kaftin Ibrahim Traoré, wanda shi ne shugaban ƙungiyar a halin yanzu, shi ne ya sanya hannu a kan sanarwar.

Ya gana da Maduro a Moscow bara a yayin bukukuwan da aka shirya don tunawa da cika shekaru 80 tun bayan nasarar Rasha kan Jamus ta Nazi.

'Tsoma baki da ba za a yarda da shi ba'

Sanarwar ta kira shawarar Shugaban Amurka Donald Trump na kama Maduro 'tsoma baki da ba za a yarda da shi ba' da kuma 'aikata cin zarafi', tare da bayyana 'goyon baya ga mutanen Venezuela, wanda aka take musu 'yancin su na kasa'.

Sojojin musamman na Amurka sun kama Maduro da matarsa a ranar Asabar a Caracas sannan suka mayar da su New York domin su fuskanci shari'a kan zargin mallakar miyagun ƙwayoyi da makamai.

Maduro ya musanta laifin a yayin da aka gabatar da shi a kotu ranar Litinin, yana cewa an 'sace shi'.