| Hausa
SIYASA
3 minti karatu
Turkiyya da Amurka sun nuna amincewa don ɗage takunkuman fannin tsaro a ganawarsu a Washington
Hakan Fidan da Marco Rubio sun tattauna kan sake shigar da Turkiyya cikin shirin F-35 da kuma ɗage takunkuma CAATSA, tare da tattaunawa mai ƙarfi don magance matsalolin.
Turkiyya da Amurka sun nuna amincewa don ɗage takunkuman fannin tsaro a ganawarsu a Washington
Bangarorin biyu sun kuma tattauna kan shirye-shiryen ziyarar shugabannin kasashen a nan gaba. / AA

Wata majiya daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta bayyana cewa, Turkiyya da Amurka sun nuna sha’awar cire takunkuman da ke kawo tarnaƙi wajen samun hadin-kai a fannin masana’antar tsaro bayan tattaunawa tsakanin manyan jami’an diflomasiyyar ƙasashen biyu na NATO.

A cewar majiyar, duka ɓangarorin biyu sun bayyana ƙudurinsu na siyasa a fili na cire takunkuman da ke hana samun hadin-kai a fannin masana’antar tsaro yayin taron da aka yi ranar Talata tsakanin Hakan Fidan da Marco Rubio a birnin Washington.

Manyan jami’an diflomasiyyar sun kuma tattauna kan batutuwan da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da takwaransa na Amurka Donald Trump suka tattauna a wata hira ta waya a ranar 16 ga Maris.

Haka kuma, jami’an biyu sun tattauna kan ziyarce-ziyarce na manyan jami’ai da za a yi nan gaba tsakanin ƙasashen biyu.

“Za a gudanar da tattaunawa mai muhimmanci don warware matsalolin da ake da su,” in ji majiyar.

Batun F-35

A ranar Talata, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya fara wata ziyara ta kwanaki biyu a Washington, wanda ita ce ziyararsa ta farko a karkashin gwamnatin Shugaba Donald Trump.

Ana sa ran zai bukaci a cire takunkuman da aka ƙaƙaba wa Turkiyya da kuma sake shigar da kasar cikin shirin jiragen yaƙi na F-35.

A wa’adinsa na farko, Trump ya yi watsi da shawarar masu ba shi shawara na sanya takunkumi kan Turkiyya bisa dokar CAATSA saboda sayen tsarin makamai na S-400 daga Rasha a shekarar 2019.

Sai dai daga baya ya dauki matakin ƙaƙaba takunkuman a shekarar 2020.

Wannan abu ya kuma janyo cire Turkiyya daga shirin cinikin jiragen F-35, inda ta kasance mai ƙerawa da kuma mai saye.

Ankara ta ce cire ta daga shirin ba adalci ba ne kuma ba ya kan doka ba, tana kuma neman a sake shigar da ita ko kuma a biya ta diyya kan jarin da ta zuba a shirin.

Neman kyautata dangantaka

Dangantaka tsakanin Amurka da Turkiyya ta kauce daga kasancewa abokan hulɗa na tsara dabaru a ‘yan shekarun nan yayin da saɓani tsakanin kasashen biyu masu dogon tarihi ya ƙara tsananta.

Gwamnatin tsohon Shugaba Joe Biden ta yi nesa-nesa da Turkiyya saboda abin da take gani a matsayin kusancin ƙawar tata ta NATO da Rasha.

Tattaunawa tsakanin abokan hulɗa kan warware matsalar S-400 ta ci gaba a karkashin Biden, amma ba a samu wani ci gaba ba.

Ziyarar Fidan ta zo ne yayin da Ankara ke neman kyautata dangantaka da Washington a karkashin wa’adin Trump na biyu.

Tun bayan komawarsa ofis a ranar 20 ga Janairu, Trump ya sauya manufofin Biden na ware Moscow da bayar da cikakken goyon baya ga Kiev, inda ya mayar da hankali kan kawo ƙarshen yaƙin Rasha a Ukraine.

Jami’in na Turkiyya ya ce tattaunawa tsakanin Washington da Ankara sun “ɗauki sabon salo” bayan sauyin da Trump ya yi wajen mu’amala da Moscow.

Sauyin da Trump ya yi ya kuma tayar da hankalin shugabannin Turai, wadanda ke tsoron cewa Washington na iya juya baya ga Turai, tare da ƙarfafa rawar Ankara a matsayin abokiyar hulɗa mai yiwuwar sake fasalin tsaron Turai.