Masu kula da ayarin jiragen ruwa masu dauke da kayan agaji da masu goyon bayan Falasɗinu zuwa Gaza sun bayyana a daren Litinin cewa ɗaya daga cikin jiragensu ya fuskanci wani hari da ake zargin jirgi mara matuƙi (UAV) ya kai a kusa da gabar tekun Tunisiya, amma hukumomin ƙasar sun ce ba a gano wani jirgi mara matuƙi ba.
Jiragen ruwan, waɗanda ke da niyyar karya takunkumin da Isra'ila ta sanya wa Gaza, sun isa Tunisiya a ƙarshen mako kuma sun tsaya a bakin gaɓar Sidi Bou Said lokacin da suka bayar da rahoton wannan lamarin.
"Kungiyar Ayarin Jiragen Ruwan Global Sumud Flotilla (GSF) ta tabbatar cewa ɗaya daga cikin manyan jiragenmu... ya fuskanci abin da ake zargin jirgi mara matuƙi ne ya kai hari," in ji masu kula da ayarin a shafukan sada zumunta, suna ƙara da cewa babu wanda ya ji rauni.
Sun yaɗa bidiyon kyamarar tsaro daga jirgin inda za a iya jin sautin wani abu yana yin ƙara, kafin wani haske ya bayyana a cikin bidiyon.
Jirgin yana cikin ruwan Tunisiya lokacin da wuta ta tashi a cikin jirgin, amma an kashe ta cikin gaggawa, a cewar wani ɗan jaridar AFP da ya isa wurin jim kaɗan bayan an kashe wutar.
‘Ba a gano jirgi mara matuƙi ba’
Amma dalilin tashin wutar ya kasance abin muhawara, inda kakakin rundunar tsaron ƙasa ta Tunisiya, Houcem Eddine Jebabli, ya ce "ba a gano wani jirgi mara matuƙi ba."
"A cewar binciken farko, wuta ta tashi ne a cikin rigunan iyo na hana nutsewa a ruwa da ke cikin jirgin," kamar yadda ya shaida wa AFP, yana mai cewa ana ci gaba da bincike.
Rahotannin da ke cewa jirgi mara matuki ne ya kai hari "ba su da tushe," in ji rundunar tsaron ƙasa a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin Facebook ɗinta na hukuma, tana nuna cewa wataƙila sigari ce ta haifar da wutar.
Wani ɗan gwagwarmaya daga Brazil, Thiago Avila, ya wallafa bidiyo a Instagram inda wani mamba daga cikin jiragen ya yi ikirarin ganin jirgi mara matuƙi.
"Tabbas jirgi mara matuƙi ne ya jefa bam," in ji mamban a cikin bidiyon.
Rundunar sojin Isra'ila ba ta amsa tambayar da AFP ta yi mata ba nan take.
Fitattun mutane da ke cikin tawagar
Ayarin Global Sumud ya bayyana kansa a matsayin wata kungiya mai zaman kanta da ba ta da alaƙa da kowace gwamnati ko jam'iyyar siyasa. Sumud na nufin "juriya" a Larabci.
Daga cikin fitattun mahalarta akwai Greta Thunberg, wadda ta yi jawabi ga masu goyon bayan Falasɗinu a Tunisiya a ranar Lahadi.
Isra'ila ta riga ta hana ƙoƙarin masu gwagwarmaya har sau biyu don kai kayan agaji ta jirgin ruwa zuwa Gaza, a watan Yuni da Yuli.
Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana yanayin yunwa a wasu sassan Gaza, tana gargadin cewa mutane 500,000 na cikin mummunan yanayi mai tsanani.










