An kashe mutum 64, cikinsu har da ƙananan yara 13, a harin asibitin Sudan — WHO

Shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce mutum 89 sun jikkata, ciki har da ma'aikatan lafiya takwas.

By
Ghebreyesus ya ce mutum 89 sun jikkata, ciki har da ma’aikatan kiwon lafiya takwas. / Reuters

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya ce ƙananan yara 13 suna cikin mutum aƙalla 64 da aka kashe a hari ta sama da aka kai wani asibiti a Sudan.

"WHO ta tabbatar da kai hari a wata cibiyar kiwon lafiya a Sudan. Wannan karon, an kai harin ne a Asibitin Koyarwa na El-Daein da ke Gabashin Babban Birnin Darfur, inda aka kashe aƙalla mutum 64, ciki har da ƙananan yara 13, da ma’aikatan jinya mata biyu da likita ɗaya da kuma marasa lafiya da dama," in ji shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus a saƙon da ya wallafa a shafinsa na X.

Ya ƙara da cewa wannan hari a asibiti ya sa yanzu adadin cibiyoyin kiwon lafiya da aka kai wa hare-haren sun zarta 2000 jimilla.

Ghebreyesus ya ce mutum 89 sun jikkata, ciki har da ma’aikatan kiwon lafiya takwas.

'Tasiri na tsawon lokaci'

WHO ta ce harin da aka kai Asibitin Koyarwa na Al Deain ranar Jumma’a ya lalata shi ta yadda ba za a iya gudanar da ayyuka ba, lamarin da zai shafi harkokin kula da lafiya a birnin.

Baya ga mutuwar mutane, Ghebreyesus ya yi gargaɗin cewa harin da aka kai a asibitin da ma’aikatan kiwon lafiya "zai yi matuƙar tasiri nan-take da kuma nan gaba kan al’ummomin yankin waɗanda dama suna cikin matsananciyar buƙatar agajin gaggawa da kula da lafiyarsu."

"An zub da jini fiye da ƙima. An jikkata jama’a. Lokaci ya yi da ya kamata a kawo ƙarshen rikicin Sudan tare da tabbatar da tsaron lafiyar fararen-hula da ma’aikatan kiwon lafiya da ma’aikatan gaggawa," in ji shi.

"Bai kamata a riƙa kai hari kan cibiyoyin kiwon lafiya ba. Zaman lafiya shi ne babban magani."