| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Ghana ta kai ƙorafi ga MDD bayan makami mai linzami ya jikkata sojojinta a Lebanon
Ministan Harkokin Wajen Ghana, Samuel Okudzeto Ablakwa, a wata sanarwa ya bayyana cewa harin da aka kai wa sojojin Ghana da ke Aikin Wanzar da Zaman Lafiya a Lebanon a ranar Juma'a ya sa sojoji biyu sun ji "rauni mai tsanani".
Ghana ta kai ƙorafi ga MDD bayan makami mai linzami ya jikkata sojojinta a Lebanon
Gwamnatin Shugaba John Mahama na neman a gudanar da bincike kan harin da aka kai wa sojojinta da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Lebanon / Reuters
8 Maris 2026

Ghana ta miƙa ƙorafi ga Majalisar Ɗinkin Duniya kan harin da aka kai wa sojojinta a Lebanon, tana neman a gudanar da bincike "cikakke, na gaggawa, kuma a bayyane".

Ministan Harkokin Wajen Ghana, Samuel Okudzeto Ablakwa, a wata sanarwa ya bayyana cewa harin da aka kai wa sojojin Ghana da ke Aikin Wanzar da Zaman Lafiya a Lebanon a ranar Juma'a ya sa sojoji biyu sun ji "rauni mai tsanani".

"Gwamnatin Ghana a hukumance ta miƙa ƙorafinta ga Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya António Guterres biyo bayan munanan hare-haren da aka kai wa sojojin wanzar da zaman lafiya na Ghana a Lebanon," in ji ministan wajen a ranar Asabar.

"Muna neman a gudanar da bincike cikakke, na gaggawa, mara ɓangaranci kuma a bayyana kan harin, wanda ya keta dokar ƙasa da ƙasa kuma ya kai ga aikata laifin yaƙi. Za mu bi diddigi domin neman adalci da kuma ƙara kariya ga jaruman sojojinmu," in ji Ablakwa.

Ya tabbatar wa waɗanda suka ji rauni da cewa suna tare da "soyayyar ‘yan ƙasa da addu'o'in al'umma, da cikakken goyon baya".

An ruwaito cewa an kai hari ga sojojin na Ghana da makami mai linzami yayin da rikici da ke ta'azzara a Gabas ta Tsakiya ya ƙaru.

Babu cikakken tabbaci kan wanda ya harba makami mai linzamin kan sojojin na Ghana, kuma ko dagangan ne aka kai musu harin. Sai dai hukumomin Lebanon sun ce Isra'ila ce ta harba makami mai linzamin.

Ayyukan rundunar

Yayin da ta sake tabbatar da jajircewarta ga ayyukan tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, kasar Afirka ta Yamma ta yi kira cewa da cewa "dole ne tsaro da kare ma'aikatan wanzar da zaman lafiya ya kasance a gaba a kokarin hadin gwiwa na kiyaye zaman lafiya da tsaro na duniya."

Rundunar Wanzar da Zaman Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Lebanon (UNIFIL) an kirkiro ta ne asali a 1978 don tabbatar da ficewar Isra'ila daga Lebanon, dawo da zaman lafiya da tsaro a duniya, da taimaka wa Gwamnatin Lebanon wajen dawo da ikonta na aikace-aikace a yankin da abin ya shafa.

Bayan ƙaruwar tashin hankalin tsakanin Isra'ila da Hezbollah a 2006, Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya inganta rundunar kuma ya faɗaɗa ƙudurorinta don haɗawa da sa ido kan dakatar da rikici da kuma tallafa wa sojojin Lebanon yayin da suke tura dakarunsu a fadin kudancin Lebanon don samr da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

An kuma ba ta aikin tabbatar da samun damar jin kai ga al'ummomin farar-hula da kuma komawar waɗanda suka tsere cikin son rai da aminci.

Rundunar tana da fiye da sojoji 7,000 waɗanda aka ɗauko daga ƙasashe da dama a ƙasar bisa ƙididdigar lissafi Disambar 2025, baya ga ma'aikata farar-hula, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.