'Rikici mafi girma a duniya': Kusan mutum miliyan 9.5 sun zama 'yan gudun hijira a Sudan — UNICEF
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa ba a bayar da cikakkun bayanai game da rikicin Sudan kuma ba a bayar da taimako yadda ya kamata, abin da ke kawo cikas ga masu gudanar da ayyukan jinƙai don biyan matsanantun buƙatun da ke ƙaruwa.
Asusun Tallafawa Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa rikicin Sudan ya zama mafi girma da ya tilasta wa mutane barin matsugunansu a cikin ƙasa inda aka ƙiyasta cewa mutane miliyan 9.5 a jihohi 18 na faɗin ƙasar sun zama ‘yan gudun hijira a rikicin shekaru uku da ake ci gaba da yi.
“A tsawon kusan shekaru uku, yara ƙanana na Sudan na gwagwarmaya da buƙatar gaggawa da rikicin ya janyo, tsugunarwa, cututtuka da yunwa a ko’ina,” in ji Asusun UNICEF a wata sanarwa.
UNICEF ya ce suna ci gaba da ayyuka a ƙasar tare da abokan hulɗa don kuɓutar da rayukan yara da iyalan da yaƙin ya shafa, ciki har da kula da lafiya da cimaka, samar da ruwan sha mai tsafta, taimako na lafiyar ƙwaƙwalwa da ilimi.
Sai dai kuma, Asusun UNICEF ya yi gargaɗi ba a bayar da cikakkun bayanai game da rikicin Sudan kuma ba a bayar da taimakon yadda ya kamata, abin da ke yin cikas ga masu gudanar da ayyukan jinƙai don biyan matsanantun buƙatun da ke ƙaruwa.
UNICEF ta jaddada cewa yara ƙanana ne suka fi cutuwa daga rikicin, tana mai jaddada buƙatar samar da zaman lafiya mai ɗorewa a faɗin ƙasar.
Tun watan Afrilun 2023, sojojin Sudan da mayaan RSF suke gwabza yaƙi da duk wata tattaunawa ta yanki da ƙasa da ƙasa ta gaza kawo ƙarshen sa. Rikicin ya yi ajalin dubban mutane.