| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
An buɗe Gasar Kofin Duniya ta 2026 inda Mexico ta lallasa Afirka ta Kudu 2-0 a Estadio Azteca
Julian Quinones da Raul Jimenez su ne taurarin Mexico a wasan yayin da Afirka ta Kudu ta gaza jefa ƙwallo ko ɗaya a wasan buɗe Gasar ta Kofin Duniya a birnin Mexico City.
An buɗe Gasar Kofin Duniya ta 2026 inda Mexico ta lallasa Afirka ta Kudu 2-0 a Estadio Azteca
An bai wa Afirka ta Kudu jan kati guda biyu, kuma suka rage 'yan wasa 9 a rabi na biyu. / Reuters

An fara Gasar Cin Kofin Duniya inda ƙasar Mexico ɗaya daga masu masaukin baƙi ta fara wasan da ƙafar dama, ta doke Afirka ta Kudu 2-0 a gaban magoya baya 80,000 a filin wasa na Estadio Azteca a birnin Mexico City.

Julian Quinones ne ya fara zura ƙwallo a minti na tara da take leda a wasan buɗe gasar a ranar Alhamis, abin da ya tabbatar da yadda Mexico ta riƙe wasa tun farko a cikin filin da aka buga wasannin ƙarshe na 1970 da 1986.

Raul Jimenez ya zura ƙwallo ta biyu ga Mexico. Bayan wakiltar tawagar Mexico a Gasar Kofin Duniya sau huɗu, a ƙarshe ya samu wannan ƙwallo ta farko da ya daɗe yana nema.

Fara wasan ya ƙaddamar da wata gagarumar gasar da ke da ƙasashe 48 wacce za ta ɗauki kusan makonni shida.

Manyan nune-nunen bikin buɗe gasar da Amurka, Mexico da Kanada masu masaukin baƙi suka gudanar shi ne mafi girma a tarihin Gasar Kofin Duniya. Za ta ci gaba har zuwa wasan ƙarshe a New Jersey a ranar 19 ga Yuli, kuma ana hasashen za ta samar da kuɗaɗen shiga da ya kai dala biliyan 13 gaba ɗaya.

Bikin buɗe gasar ya haska filin wasa na Estadio Azteca kafin fara wasan, inda tauraruwar Colombia Shakira da mawakin Nijeriya Burna Boy suka nishaɗantar da ‘yan kallo da rera "Dai Dai", waƙar gasar a hukumance.

Amma an samu turereniya a wajen filin, yayin da magoya baya ke dannawa da tura juna suna ƙoƙarin shiga yankin da aka ware wa magoya baya a tsakiyar birnin Mexico.

Tururuwar da aka yi wajen shiga filin wasan zai kasance abin da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya FIFA za ta yi farin ciki da shi, wadda ta fuskanci suka mai tsanani kan tsadar tikiti.

Rumbun Labarai
Shugaban Amurka Donald Trump ya gargaɗi FIFA a kan maye gurbin Infantino
Manyan hukumomin ƙwallon ƙafa na zargin shugabancin FIFA da ‘cin amana’
Mohamed Salah ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyu da Trabzonspor ta Turkiyya
Danwasan Chelsea, Mudryk, ya dawo kwallo bayan dakatarwar kwana 600 bisa laifin shan kwayoyin kuzari
Arsene Wenger ‘ba shi da masaniya’ kan shirin Infantino na sayar da hannun-jarin Gasar Kofin Duniya
FIFA ta gaza hukunta Isra'ila kan karya dokokinta, a cewar hukumar Kwallon Kafa ta Falasɗinu
Masu adawa da Infantino sun yi barazanar gudanar da gasar kofin duniya ba a karkashin FIFA ba
WAFCON: Tawagar Super Falcons ta Nijeriya mai 'yanwasa 10 ta doke Zambia
Infantino ya ce FIFA ta fasa shirin sayar da hannayen-jari na Kofin Duniya ga ‘yan kasuwa
FIFA ta ce 'babu wanda zai sayar da ƙwallon ƙafa'
UEFA ta sha alwashin ƙaurace wa FIFA idan aka ci gaba da shirin sayar da Gasar Kofin Duniya
Infantino ya goyi bayan ƙudurin saka hannun jari na FIFA, ya ce 'dama ce ta musamman'
UEFA ta soki shirin Infantino na $4.2bn don zuba jari a Gasar Kofin Duniya ta FIFA
An nada Zinedine Zidane a matsayin sabon kocin tawagar kwallon kafa ta Faransa
Yan Diomande ne zai kasance dan Ivory Coast na farko da zai buga wa Real Madrid wasa
Real Madrid ta sanya fam miliyan 137 kan Vinicius Junior
Lamine Yamal: Gwarzon Kofin Duniya na Spain ɗan asalin Moroko da Equatorial Guinea
Norway za ta shigar da ƙara ga hukumar FIFA game da ce-ce-ku-ce kan jan katin Balogun
Real Madrid na farautar zakaran kofin duniya Ferran Torres daga wajen Barcelona
Yadda goyon bayan Falasɗinu ya haɗa kan Musulmai suka goyin bayan Spain a Gasar Kofin Duniya na 2026