| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
An yanke wa tsohon kwamandan Taliban hukuncin shekara 42 a kurkukun Amurka kan garkuwa da mutane
Wata kotun New York ta ɗaure Haji Najibullah, wani tsohon kwamandan Taliban bisa rawan da ya taka a garkuwa da wani ɗanjaridan Amurka da wasu 'yan ƙasar Afghanistan biyu tare da goyon bayan hare-haren kashe jami'an sojin Amurka a Afghanistan.
An yanke wa tsohon kwamandan Taliban hukuncin shekara 42 a kurkukun Amurka kan garkuwa da mutane
Wannan shi ne danjaridar da tsohon kwamandan Taliban din ya taba sacewa. / AP

Wata kotun Amurka ta yi wa wani tsohon kwamandan Taliban ɗaurin shekaru 42 ranar Talata da kuma shekara biyar na saki da sa ido domin rawar da ya taka wajen garkuwa da mutane, ciki har da wani ɗanjaridar Amurka, wanda aka bayyana sunansa a matsayin ɗanjarida David Rohde na Jaridar New York Times .

Wata kotun New York ce ta yi wa Haji Najibullah mai shekara 50 din ɗaurin domin “rawar da ya taka wajen kama wani ɗanjaridar Amurka da ‘yan Afghanistan biyu a Afghanistan da Pakistan a shekarar 2008 da 2009,” kamar yadda wata takardar koru ta bayyana.

An kuma ɗaure shi sakamakon rawar da ya taka wajen jagorantar mayaƙan Taliban da suka ƙaddamar da hare-hare kan jami’an sojin Amurka a Afghanistan tsakanin shekarar 2007 da shekarar 2009, lamarin da ya haddasa mace-macen sojojin Amurka.

Bayan an kama shi a ƙasar Yukraine, an mayar da shi zuwa Amurka a shekarar 2020.

An kama shi ne ranar 25 ga watan Afrilun shekarar 2025, sannan Najibullah ya amsa laifin garkuwa da mutane da kuma ba da taimako na kaya ga ayyukan ta’addanci da suka haddasa mutuwa, in ji takardar.

“Waɗanda suka ji wa Amurkawa ciwo kuma suka taka rawa a ta’addanci za mu yi farautarsu da kuma gurfanar da su a gaban kotu, komin daɗewa,” in ji muƙaddashin Antoni Janar Todd Blanche, kamar yadda takardar ta ambato.

“A matsayinsa na kwamandan Taliban, Najibullah ya taimaka wa hare-haren ta’addanci mara tausayi da suka kashe jami’an sojin Amurka da kuma kitsa garkuwa da mutane mara tausayi kan wani ɗanjarida Ba’amurke da fararen hula ‘yan Afghanistan biyu.

Ɗaurin yau ya ba da hukuncin gaskiya ga waɗanda lamarin ya rutsa da su da iyalansu.”

An yi garkuwa da Rohde ne a ƙasar Afghanistan cikin watan Nuwamban shekarar 2008, tare da wani tafinta da wani direba.

Jaridar Times, ta samu ta ɓoye labarin garkuwa da shi domin kada ta yi barazana ga rayuwarsa, inda Rohde ya samu ya tsere daga wadanda suka yi garkuwa da shi a watan Yunin shekarar 2009.

Rumbun Labarai
Gobarar daji a jihar Washington ta Amurka ta tilasta wa dubban mutane tserewa
Jirgin yaƙin Amurka samfurin F-35 ya faɗi kusa da wani sansanin soji
Tarayyar Turai ta yi kira da a zartar da umarnin Kotun ICC na kamo Netanyahu
Macron ya ce Faransa na fama da gobarar daji mafi muni da ba a taɓa ganin irinta ba
Turai na babbakewa: Me muka sani zuwa yanzu?
Faransa da Sifaniya na fama da mummunar gobarar daji
Yadda kujerar Firaministan Birtaniya ke komawa tamkar kujerar aski
Trump ya ce ba za a yi yarjejeniyar nukiliya da Saudiyya ba sai ta amince da gyara alaƙa da Isra'ila
Trump ya tarbi gawawwakin sojojin Amurka da aka kashe a yaƙin Iran
Trump ya amince da yarjejeniyar shirin nukiliya na farar-hula da Saudiyya — Rahoto
Sabon Firaministan Birtaniya Burnham ya yi alƙawarin rage tsadar rayuwa
Netanyahu ya fusata Trump bayan ya caccaki shirin Amurka na sayar wa Turkiyya F-35: Rahoto
Ana fargabar mutuwar 'yan ƙabilar Rohingya fiye da 500 bayan kifewar jiragen ruwa a gaɓar Myanmar
Masu ceton dabbobi na taimaka wa tsuntsaye tsira daga bazara mai zafi
Ƙirkirarriyar Basira, ƙarfin intent da ƙa’idojin aikin jarida
Yawan masu kamuwa da cutar kansa na iya kusan ninkuwa nan da shekarar 2050
Mai tsaron bayan Argentina ya ce alƙalan wasan Gasar Kofin Duniya 'na aiki mai kyau'
An kona gini mai kama da masallaci a Arewacin Ireland  a yayin da ‘yansanda ke gudanar da bincike
An samu rahotannin cin zarafin mata kusan 9,800 a shekarar 2025, fiye da ninki biyu kan na 2024: MDD
Mene ne takunkuman CAATSA kuma ta yaya cire su da Amurka za ta yi zai amfani Turkiyya?