| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Yadda na tsira daga kifewar jirgin Sokoto da ya kashe mutum fiye da 60—Hakimi
Aliyu Magaji ya ce da shi ya sake tasowa, ya ji wasu sun sake riƙe shi sai ya sake nustewa, kuma daga baya ya harba wani wuri daban.
Yadda na tsira daga kifewar jirgin Sokoto da ya kashe mutum fiye da 60—Hakimi
Aliyu Magaji, Hakimin Gorau, ya bayyana yadda ya tsira daga kifewar kwale-kwale a ƙramar hukumar Goronyo na jihar Sokoto / Facebook/Iconic FM

Ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira daga kifewar jirgin ruwa a garin Gorau da ke ƙaramar hukumar Goronyo ta jihar Sokoto a arewa maso yammacin Nijeriya, Aliyu Magaji Gorau wanda shi ne hakimin garin ya yi ƙarin haske game da yadda lamarin ya auku da adadin waɗanda suka rasu sakamakon hatsarin.

A wata hira da yi da gidan rediyon Iconic FM a ƙasar hakimin ya ce jirgin ya kwashe ruwa ne kafin ya kife da mutane ranar Alhamis.

“A cikin jirgin ni kaɗai ne babba, bayan matuƙin jirgin ni kaɗai ne babba. To a lokacin da ya kwashi ruwa, duk mutanen da ke ciki ni suka zaburo suka riƙe ni. Ban iya kufce musu ba. Illa dai iyaka da na samu nima na nutse sai na zage kayana sai na bar su da su,” in ji hakimin.

Aliyu Magaji ya ce da shi ya sake tasowa, ya ji wasu sun sake riƙe shi sai ya sake nustewa, kuma daga baya ya harba wani wuri daban.

“To akwai buhun tonka wanda shi na samu da taimakon Allah na samu na dafa na fita. Saura kam ban san yadda aka yi ba,” in ji shi.

Da ya iso bakin ruwa, mutane sia suka taimaka suka kai shi gefe inda ya shafe wajen sa’a ɗaya bai san ma me ake yi ba.

Kuma daga  baya ne aka saka babur ya kai shi cikin garin.

“Kafin dai La’asar jiki na ya dawo, kuma muka koma bisa al’aumura. To a lokacin dai an tsamo wajen mutane wajen 48 waɗanda an ka yi jana’izarsu. Kuma an ci g ba da .. yanzu muna da wajen mutum 62 waɗanda aka rufe (binne). Kuma ana nan ana ci gba ada bincike har yanzu,” a cewarsa.

Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya umarci hukumar da ke kula da sufurin cikin ruwa a cikin ƙasar NIWA da  hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasar NEMA su yi aiki da gwmamnatin jihar Sokoto domin kauce wa sake aukuwar lamarin da kuma tabbatar da cewa ana ɗabbaka matakan tsaro kan hanyoyin ruwa.

Hatsarin ya faru shekara ɗaya bayan an yi irinsa a garin Kijiyo a ƙaramar hukumar ta Goronyo.