| Hausa
AFIRKA
1 minti karatu
Shugaba Tiani na Nijar ya nada Aboubacar Issaka a matsayin sabon shugaban ’yansandan kasar
Shugaba Janar Abdourahamane Tiani, ya naɗa sabon shugaban rundunar ’yan sandan ƙasar tare da mataimakinsa a wasu dokoki gida biyu da ya saka wa hannu.
Shugaba Tiani na Nijar ya nada Aboubacar Issaka a matsayin sabon shugaban ’yansandan kasar
Issaka Oumarou Nijar / Others

Shugaban Nijar Janar Abdourahamane Tiani, ya naɗa sabon Darakta Janar da Mataimakinsa na rundunar ’yan sandan ƙasar.

An sanar da naɗe-naɗen ne ta hanyar wasu dokokin shugaban ƙasa guda biyu da aka sanya wa hannu ranar Juma’a, 13 ga Nuwamban 2026.

An naɗa Kwamishinan ’Yansanda Janar Aboubacar Issaka Oumarou a matsayin Darakta Janar na rundunar ’yansandan ƙasar, yayin da aka naɗa kwamishinan ’yansanda na sashen Abdoulaye Maman Mijinyawa a matsayin mataimakinsa.

Kafin wannan naɗi, Oumarou ya taɓa shugabantar Hukumar Yaƙi da Safarar Miyagun Ƙwayoyi ta Nijar (OCRTIS).

Dokokin naɗin sun bayyana cewa ministocin harkokin cikin gida, tsaron jama’a da kula da harkokin yankuna, da kuma tattalin arziki da kuɗi, su ne za su tabbatar da aiwatar da naɗe-naɗen bisa ikon ma’aikatunsu.