'Masu gurɓataccen ra'ayi': Me ya sa ƙaruwar gudunmawar Turkiyya a NATO ke kaɗa hantar Isra'ila?
Ƙasar Isra'ila ta haddasa fitina a Gabas ta Tsakiya, daga Gaza zuwa Lebanon da Syria da Yemen inda a yanzu Iran. Haka kuma tana yawan adawa da yunƙurin da Ankara ke yi na samar da zaman lafiya a matsayinta na mamba a NATO/
A cikin shekaru uku da suka gabata, Isra'ila ba kan Falasɗinawa kawai ta kai hari ba, har ma da wasu ƙasashen da ke Gabas ta Tsakiya waɗanda suka haɗa da Lebanon zuwa Syriya, Yemen sai kuma kwanan nan Iran — abin da ya ƙara fito da sunanta a matsayin mai tayar da tarzoma a wannan yankin mai tashin hankali.
Yayin da Turkiyya wadda mamba ce a NATO, tun da daɗewa take neman warware matsaloli cikin lumana don kawo ƙarshen rikice-rikice daban-daban daga Ukraine zuwa Gaza da Iran, sai dai Isra'ila tana ƙoƙarin yin kowace irin dabara ta sharri don rushe ƙoƙarin Ankara na neman zaman lafiya.
“Muguwar aniyar Isra'ila kan Turkiyya ta ƙara tsananta musamman cikin shekarun biyu da suka gabata, tana aika sakonnin yaƙi ga Ankara da murya ta soja,” in ji Gokhan Batu, mai fashin baƙi kan siyasa da kuma harkokin Isra’ila da Gabas ta Tsakiya wanda ke zaune a Ankara, yana nuni ga ƙarin tashin hankali a yankin tun 7 ga Oktoban, 2023.
Tun bayan da Tel Aviv ta fara yakin kisan kiyashi a Gaza, wanda ya kashe ɗaruruwan dubban mutane kuma ya mayar da yankin Falasdinu zuwa ɓaraguzai, Turkiyya ta kasance ɗaya daga cikin waɗanda suke caccakar Isra’ila a kan hakan.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yana fuskantar ƙarin bincike a duniya, inda har Kotun Duniya ta bayar da umarnin tsare shi.
Haka kuma a cikin gida yana fuskantar ƙarin zargin da suka fito daga shugabannin siyasa, jami'an soja da jama'a waɗanda ke nuna fushinsu saboda amfani da yaƙe‑yaƙe a matsayin hanyar tsira na siyasa.
Batu ya ce dole ne a fahimci ƙaruwar ƙiyayyar da Isra’ila ke nuna wa Turkiyya ta fuskar sauye‑sauyen siyasar duniya na baya‑bayan nan.
“Za a fi fahimtar irin wannan halayya ta Isra’ila idan an sanya ta cikin mahangar bunƙasar Turkiyya a Gabas ta Tsakiya da fitowarta a matsayin wanda za ta iya fito-na-fito da Isra’ila a yankin,” in ji Batu ga TRT World.
Batu ya ce haɓakar masana'antar tsaron Turkiyya wadda ta samu nasarori — daga jiragen sama marasa matuƙa na zamani zuwa ƙaruwa a ƙarfin jiragen ruwa wanda wasu ƙasashe kamar Italiya suka yi koyi da su — na sa gwamnatin Netanyahu mai tsattsauran ra'ayi tashin hankali.
Turkiyya za ta karbi bakuncin wani muhimmin taron kolin NATO a wannan bazarar, inda haɗin gwiwar ƙasashen Yamma zai samu damar nazarin ƙaruwa a cikin damuwar siyasa ta duniya a tsakanin rikice‑rikice daga Gabashin Turai zuwa Gabas ta Tsakiya.
Turkiyya, wadda ita ce ta biyu a girman sojoji a NATO, kwanan nan ita da Birtaniya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro, abin da ya zama wata shaida ta jan hankalin tsaron Ankara ga abokan kawancenta na Yamma.
Dalilin da yasa NATO ke muhimmanci
Isra'ila ba ta jin daɗi da kasancewar Turkiyya a NATO, abin da ke hana Tel Aviv daga yin adawa kai tsaye ga ƙaruwar kasancewar Ankara a fannoni daban‑daban, daga Libya zuwa Somalia da Syria, in ji Ali Burak Daricili, farfesa a sashen dangantakar ƙasashen waje na Jami'ar Fasaha ta Bursa.
Duk da ayyuka masu tsanani na shugabancin Isra'ila na yanzu wanda Daricili ya kwatanta a matsayin “mai tsattsauran ra'ayi na addini mara hankali, Turkiyya za ta ci gaba da zama mai yin siyasa mai hankali, tana mayar da martani kan tsokanar gwamnatin Netanyahu a yankuna daban‑daban a “hankalce,” in ji Daricili ga TRT World.
Yayin da Turkiyya ke ƙoƙarin kare ƙasar Somalia ta hanyar shiga tsakani, tsakanin Somalia da Ethiopia don taimaka wa magance bambance‑bambancen da ke tsakanin waɗannan ƙasashen Gabashin Afirka, Isra'ila na nufin rushe zaman lafiyar yankin ta hanyar amincewa da yankin Somaliland mai neman rabewa a matsayin ƙasa mai 'yanci.
Kamar a Gabashin Afirka, Turkiyya ma ta yi aiki tukuru don hana da rage girman yakin a Iran.
Haka kuma a Syria, yayin da Isra'ila ke ci gaba da tayar da bama-bamai a wurare daban‑daban da tallafawa ƙungiyoyi na kabilanci da addini kamar Druzes da mai adawa da sabon shugabanci a Damascus, Turkiyya ta taimaka wa canjin ƙasar zuwa ƙasa mai zaman lafiya tare da ƙarfi na gwamnati ta tsakiya.