Samaila Bagudo: 'Yan bindiga sun sace Mataimakin Kakakin Majalisar Jihar Kebbi
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta tabbatar da sace ɗan majalisar inda ta ce ‘yan bindiga ɗauke da makamai sun afka gidan ɗan majalisar da ke Ƙaramar Hukumar Bagudo inda suka sace shi jim kaɗan bayan ya kammala Sallar Isha’i.
‘Yan bindiga ɗauke da makamai sun yi garkuwa da Mataimakin Kakakin Majalisar Jihar Kebbi, Samaila Bagudo a gidansa.
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta tabbatar da sace ɗan majalisar inda ta ce ‘yan bindiga ɗauke da makamai sun afka gidan ɗan majalisar da ke Ƙaramar Hukumar Bagudo inda suka sace shi jim kaɗan bayan ya kammala Sallar Isha’i yana hanyarsa ta komawa gida.
‘Yan sandan sun ce tuni aka aika da jami’an tsaro domin ƙoƙarin ceto ɗan majalisar.
A cewar sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ya fitar, lamarin ya faru ne a ranar Jumma’a, 31 ga Oktoba, 2025, da misalin ƙarfe 8:20 na dare.
Sanarwar ta ce: “An tura tawagar hadin gwiwa da ta ƙunshi ‘yan sanda, sojoji, da ‘yan sa kai zuwa yankin domin aikin ceto.
“Dakarun haɗin gwiwar suna ci gaba da tantance hanyoyin da ake zargin ‘yan bindiga ke bi da dazuzzukan da ke kewaye, domin ceto dan majalisar ba tare da wani rauni ba, da kuma kama waɗanda ke da hannu a harin.”
Sanarwar ta ƙara da cewa kwamishinan ‘yan Sanda ya sake tabbatar da kudirin rundunar wajen kare rayuka da dukiyoyi a fadin Jihar Kebbi, yana bayyana garkuwar a matsayin “mummunan aiki da ba za a bar shi haka kawai ba.”
Rundunar ta kuma roƙi jama’ar jihar da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu kula, tare da bayar da bayanai masu amfani da za su taimaka wajen aikin ceto da ke gudana.