Wata gobara da ta tashi a wani gidan rawa a North Macedonia ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 59 a yayin wani biki da fiye da mutum dubu suka taru a ranar Lahadi, kamar yadda ministan harkokin cikin gida na ƙasar ya tabbatar.
Tun da farko kamfanin dillancin labarai na ƙasar wato MIA ya ruwaito cewa “aƙalla mutum 50 sun rasu a wani gidan rawa a Kocani”, wanda gari ne da ke da nisan kilomita 100 daga Skopje babban birnin ƙasar inda kusan “mutum 1,500 suka halarci wani biki”.
Sai dai daga baya kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito Ministan Harkokin Wajen North Macedonia, Pance Toskovski yana cewa adadin ya ƙaru zuwa mutum 59 inda ya kuma ce an gane gawawwakin mutum 35.
Mista Toskovski ya bayyana cewa tuni aka bayar da takardar izini domin kama mutum huɗu sakamakon wannan gobarar.
Zuwa yanzu adadin waɗanda aka tabbatar sun jikkata sakamakon wannan gobarar ya kai mutum 155.
Ministan ya ce 31 cikin gawawwakin da aka gano ko su wane ne mazauna Kocani ne.
Ministan ya ce gobarar ta tashi ne sakamakon wasan tartsatsin wuta inda wutar ta kama silin ɗin ɗakin har gobara ta tashi.
Haka kuma Toskovski ya ce tuni aka aika da waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban da ke faɗin ƙasar.










