NIJERIYA
2 minti karatu
Sabon reshen Boko Haram 'Wulowulo' na aika-aika a yankin tsakiyar Nijeriya — Gwamnan Nasarawa
Gwamnan jihar Nasarawa ya ce kasancewar sabuwar ƙungiyar ta’addancin zai ta’azzara matsalar tsaro da dama ake fama da ita a yankin arewa maso tsakiyar Nijeriya.
Sabon reshen Boko Haram 'Wulowulo' na aika-aika a yankin tsakiyar Nijeriya — Gwamnan Nasarawa
Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule
15 Oktoba 2025

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya ce wani sabon reshe na ‘yan ta’addar Boko Haram da aka sani da suna ‘Wulowulo’ ya shiga yankin arewa maso tsakiyar Nijeriya.

Sule ya yi wannan bayanin ne ranar Litinin a wani taron masu ruwa da tsaki da hukumomin tsaro da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar.

Gwamnan ya ce kasancewar sabuwar ƙungiyar ta’addancin zai ta’azzara matsalar tsaro da dama ake fama da ita a yankin arewa maso tsakiyar Nijeriya.

Ya ce akwai buƙatar a ɗauki matakan tsaro domin hana sabuwar ƙungiyar shiga jihar Nasarawa.

“Kamar yadda kuka sani, wannan sabuwar ƙungiyar mai suna Wulowulo, wadda wata ƙungiya ce wadda ta ɓalle daga Boko Haram, ta fara bayyana a arewa maso tsakiyar Nijeriya,” in ji Sule.

“A halin yanzu ƙungiyar Lakurawa wata babbar matsala ce a Kwara. Asali a da suna wuraren jihohin Kebbi da Sokoto ne, amma a halin yanzu sun yi ƙaurin suna a Kwara. Kwara ɗaya ce daga cikin jihohin arewa maso tsakiyar Nijeriya.

“Ɗaya daga cikin dalilan da suka sa muka gayyace ku nan shi ne yanayin rashin tsaro, musamman a wasu sassan ƙasar nan, babban abin damuwa ne.

“Wasu daga cikinsu sun fara shiga jiharmu. Yana da mahimmanci mu ɗauki matakai domin tabbatar da cewa hakan bai faru ba.”

Gwamnan ya nuna damuwa game da yadda yawan garkuwa da mutane ke ƙaruwa a wasu sassan ƙananan hukumomin Lafia da Karu na jihar.

Ya ƙara da cewa akwai wata buƙata ta samar da sabuwar dabarar tsaro domin magance ƙaruwar yawan garkuwa da mutane da ake samu.

A ƙarshen shekarar da ta gataba, wata sabuwar ƙungiyar ta’addanci, Lakurawa ta fara shiga wasu sassan jihohin Sokoto da Kebbi daga Jamhuriyar Nijar da Mali.

 

Rumbun Labarai
An gabatar da kudiri a Majalisar Dokokin Amurka don saka wa Ƙungiyoyin Miyetti Allah takunkumi
‘Kisan kiyashi ga Kiristoci: Me ya sa kurarin Trump a Nijeriya yake kan kuskure da rashin dacewa?
Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince a ɗaure malaman makaranta shekara 14 kan cin zarafin ɗalibai
An kashe 'yan ta'adda fiye da 592 a Borno tun daga Maris din 2025 - Ministan Yada Labaran Nijeriya
ECOWAS ta yi tir da ikirarin ‘ƙarya mai hatsari’ na Amurka cewa Nijeriya ta bari ana kashe Kiristoci
Hukumar DSS a Nijeriya ta kori ma'aikatanta fiye da 100
Amurka na da ajanda a Nijeriya tana fakewa da kisan Kiristoci - Sheik Bala Lau
China na adawa da Trump kan amfani da 'addini da ‘yancin ɗan'adam' domin tsoma baki a Nijeriya
Naira da hannayen-jari Nijeriya sun faɗi sakamakon barazanar da Trump ya yi ta kai hari ƙasar
Jami'an tsaron Nijeriya sun hallaka 'yan bindiga 19 a Jihar Kano
Yadda barazanar da Trump ya yi kan aika sojoji Nijeriya ta tayar da ƙura
Dakarun Nijeriya sun kuɓutar da mutanen da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su Jihar Kogi
Ya kamata Amurka ta taimaka wa Nijeriya da makamai maimakon barazana —Kwankwaso
Muna shirin ɗaukar mataki kan Nijeriya - Sakataren Ma’aikatar Yaƙi na Amurka
Trump ya umarci Ma'aikatar Yaƙi ta Amurka ta soma shirin yiwuwar kai hari Nijeriya
Tinubu ya mayar da martani bayan Amurka ta ce ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Nijeriya
Gwamnatin Nijeriya ta sake jaddada aniyarta ta yaƙi da tsattsauran ra'ayi
Samaila Bagudo: 'Yan bindiga sun sace Mataimakin Kakakin Majalisar Jihar Kebbi
Donald Trump ya ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake yi wa Kiristoci kisan gilla
‘Yan sandan Nijeriya sun ceto ‘yan kasashen waje 23 da aka yi garkuwa da su