Alamun gargaɗi na siyasa sun fara bayyana ga ‘yan jam’iyyar Republican gabanin zaɓukan rabin wa’adi, yayin da yaƙin da ake yi a Iran ya sa farashin mai ya yi sama kuma Amurkawa suke nuna damuwa game da tsadar rayuwa.
Alama ta baya bayan nan ta zo ne daga inda Shugaba Donald Trump yake da tagomashi, inda ‘yar Democrat Emily Gregory ta lashe wani zaɓe na musamman na jihar Florida a wata gunduma da ta haɗa da gidansa na Mar-a-Lago estate.
Ƙuri’un jin ra’ayin jama’a sun nuna cewa yawancin Amurkawa sun yi imanin cewa matakin sojin Amurka kan Iran ya wuce gona da iri, yayin da masu ƙada ƙuri’a ke ƙara nuna damuwa game da tsadar rayuwa, sannan samun aiki da ke daɗa wahala ga kuma sababbin barazanar hauhawar farashi.
Trump yana nuna ba wata damuwa sosai dangane da tasirin hakan a kan tattalin arziki, yana mai bayyana shi a matsayin wani abu na taƙaitaccen lokaci.
Farashin mai ya tashi zuwa $3.98 kan galan ɗaya, daga ƙasa da $3 kafin a fara yaƙin, in ji Ƙungiyar Masu Motoci ta Amurka (AAA).
Ana tsammanin ƙarin kuɗin mai zai tayar da farashin kayayyaki a ƙasar ciki har da na kayayyakin abinci da na hidindimu.
Ƙarin matsi
Kimanin kashi 59 cikin 100 na Amurkawa sun ce hare-haren soji kan Iran sun wuce gona da iri, yayin da kashi 45 cikin 100 na Amurkawa suka nuna damuwa game da iya siyan mai, in ji wata ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a ta AP-NORC..
Ana tsammanin hauhawar farashi za ta ƙaru, yayin da masu ɗaukar mutane aiki suka sallami mutane 92,000 a watan da ya gabata.
Rufe wani ɓangare na gwamnati ya shiga makonsa na biyar, abin da ya sa aka dakatar da ayyuka a wasu filayen jiragen sama.
‘Yan Republican sun ɗaura wa alhakin hana sakin kuɗaɗe kan ‘yan Democrat, yayin da tattaunawa ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.
Trump ya kare yaƙin, yana mai cewa : "Dole na yi abin da ya dace."
Wasu ‘yan Republican sun nemi a yi haƙuri.
"Ina ganin wannan zai iya kasancewa abin da zai ƙarfafa fahimtar masu ra’ayin ‘yan mazan jiya game da yadda ya kamata a tunkari batun tsaron ƙasa," in ji ɗanmajalisa Nick LaLota.














