Shugaban ƙasar Siriya Ahmed al Sharaa ya naɗa tsohon shugaban ƙungiyar SDF/YPG Mazloum Abdi a matsayin mai ba shi shawara, a cewar kamfanin dillancin labarai na SANA.
Al Sharaa ya fitar da wata sanarwar doka a ranar Alhamis, inda ya naɗa Abdi a matsayin "mai ba da shawara ga Shugabancin Jamhuriyar," in ji SANA.
A wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata, Abdi ya sanar da cewa an wargaza ƙungiyar ta'addanci ta SDF/YPG a wani taron manema labarai.
Gwamnatin Siriya da YPG sun cim ma yarjejeniya a ranar 29 ga Janairu wadda ta tanadi tsagaita wuta da kuma shigar da ‘yanƙungiyar cikin cibiyoyin gwamnati.
A baya dai, Abdi ya taɓa zama shugaban ƙungiyar ta'addanci ta SDF/YPG.
Yarjejeniyar watan Janairu ta tanadi cewa dukkan cibiyoyin farar hula da na soja da ke ƙarƙashin ikon ƙungiyar a arewa maso gabashin Siriya - gami da waɗanda suke ɓangaren iyakoki da filayen jiragen sama da kuma na mai da iskar gas - za a haɗa su cikin tsarin gwamnatin Siriya.
Kungiyar ta'addanci ta SDF da Amurka ke marawa baya, wacce YPG reshen kungiyar 'yan ta'adda ta PKK a Siriya ta mamaye ta- a baya ta ki yarda ta haɗa kai da tsarin sojin ƙasar inda Damascus ta sha zarginta da jinkirta aiwatar da yarjejeniyar.
Turkiyya ta sha yin kira ga dukkan ƙungiyoyin ta'addanci da ke da alaƙa da PKK, ciki har da YPG/SDF, da su kwance damararsu da ajiye makamansu tare da kuma wargaza kungiyoyinsu, tana mai jaddada cewa zaman lafiyar Siriya ya dogara ne kan kawar da tsarin ta'addanci da kuma kiyaye mutuncin yankunan kasar a karkashin gwamnati ɗaya da rundunar kasa ɗaya.
Sanarwar SDF ta kawo ƙarshen ƙungiyar ta biyo bayan da PKK ta sanar da wargaza kanta a hukumance kuma ta kawo karshen yaƙinta na shekaru da dama, bayan ci gaba da ayyukan yaki da ta'addanci da sojojin Turkiyya suka yi wanda ya rage karfin aikin kungiyar tare da kawar da ikonta na aiki a cikin Turkiyya.




















