Tawagogin ƙwallon ƙafa na ƙasashen Afirka suna cikin mawuyacin hali yayin da babbar gasar ƙwallon ƙafa ta duniya, Kofin Duniya na FIFA ke ƙaratowa.
Kungiyoyi arba'in da takwas da kuma ƙasashe uku masu masaukin baƙi, wato Amurka, Mexico, da Canada suna shirin tunkarar gasar.
Ga Afirka, wannan gasar, wadda za a fara a watan Yuni, ya kamata ta kasance mai cike da tarihi, saboda nahiyar Afirka ta samu mafi girman adadin wakilci. Amma alamu na nuna akwai matsala. Kuma ga dililin
Senegal da Ivory Coast na cikin jerin ƙasashen da dokar hana tafiya ta Donald Trump ta shafa. Wannan dokar ba wai Afirka kaɗai ta shafa ba. Haka ma ta shafi Haiti, wata ƙasa ta yankin Caribbean da magoya bayanta za su iya fuskantar irin waɗannan takunkumai.
Wannan babbar matsala ce. An tsara waɗannan ƙungiyoyi su buga wasannin rukuni a Amurka. Senegal za ta fafata da Faransa a New York, yayin da Ivory Coast za ta buga da Ecuador a Philadelphia.
Magoya baya na iya kasa shiga
‘Yan wasan za su kasance a wurin, amma yawancin magoya bayansu za su iya rasa damar shiga Amurka.
Takunkumin hana biza ba shi ne kaɗai ƙalubale ba. Ta’azzarar rikici a yankin ya ƙara wani sabon mataki na rashin tabbas.
A ranar 28 ga Fabrairu, Amurka da Isra'ila sun ƙaddamar da hare-hare kan Iran. Nan take Qatar ta ɗage dukkan harkokin wasannin a watan Maris, ciki har da wasannin shiri tare da Masar da wasu ƙasashen Afirka da suka dogara da waɗannan shirye-shiryen.
Rufe sararin samaniya a wasu sassan Gabas ta Tsakiya yanzu yana kawo cikas ga hanyoyin tafiya da ƙungiyoyin Afirka da yawa ke amfani da su wajen zirga-zirga tsakanin Turai da nahiyar Arewacin Amurka.
Halin da Masar ke ciki ya fi rikitarwa. An sa su a rukuni ɗaya da Iran, ƙasar da yanzu ke cikin rikici kai-tsaye da ɗaya daga cikin ƙasashen da ke ɗaukar baƙuncin gasar, wato Amurka.
Idan wannan yanayin ya rincaɓe, Masar na iya samun kanta cikin rukunin da wasannin ba lallai su faru ba.
An matsar zuwa gefen
Wannan ba zai zama karo na farko ba da Afirka ta samu kanta a gefe guda a gasar kofin duniya.
A shekarar 1966, dukan ƙasashen Afirka sun janye daga jerin neman cancanta gasar don nuna adawa bayan FIFA ta ba Afirka, Asiya, da Oceania gurbi guda ɗaya na haɗin-gwiwa a gasar da aka yi a Ingila.
Shi ne kaɗai karon da aka buga gasar Kofin Duniya a tarih, inda nahiyar bakiɗaya ta yi ƙaurace wa gasar.
Afirka ta yi fafutukar neman wakilci. Kuma a yau tana da ƙungiyoyi tara, wato Senegal, Maroko, Tunisiya, Guinea, Aljeriya, Ghana, Cape Verde, Masar da Afirka ta Kudu.
Amma fa samun wakilci ba tare da damar halartar iyalai da magoya baya ba zai zama abin nuni kawai.










