Mayaƙan RSF kashe mutum 200 a Darfur na Sudan, ciki har da mata da yara: Likitoci

Ƙungiyar Likitoci ta Sudan Doctors Network ta ce waɗanda suka tsira ne suka bayar da rahoton kashe-kashen da mayaƙan Rapid Support Forces suka yi a samamen da suka kai Arewa da Yammacin Darfur.

By
Ƙungiyar ta ambato wasu ganau da suka tsira daga hare-haren da mayaƙan na RSF suka kai a sansanin ‘yan gudun hijira na Tina / AA

Mayaƙan Rapid Support Forces (RSF) sun kashe mutum fiye da 200, cikinsu har da mata da ƙananan yara a yankin Darfur na Sudan, a cewar wata sanarwa da ƙungiyar likitoci ta Sudan Doctors Network ta fitar ranar Asabar.

Ƙungiyar ta ambato wasu ganau da suka tsira daga hare-haren da mayaƙan na RSF suka kai a sansanin ‘yan gudun hijira na Tina, kusa da kan iyakar Sudan da Chadi, suna cewa kashe-kashen na ƙabilanci ne da aka yi a ƙauyukan Ambro da Abu Qamra a Jihar Arewacin Darfur da ƙauyen Sirba a Jihar Yammacin Darfur.

“Mutanen aka kashe sun haɗa da ƙananan yara, mata da maza waɗanda aka kai wa hare-hare da gangan saboda ƙabilanci,” in ji sanarwar, wadda ta bayyana hakan a matsayin gagarumin keta dokokin ƙasashen duniya da take hakkin ɗan’adam.

Mayaƙan RSF ba su ce komai game da wannan iƙirari ba.

Wannan lamari na faruwa ne a yayin da ake ci gaba da fafatawa a Jihar Arewacin Darfur. Rundunar Haɗin Gwiwa na Joint Force of Armed Movements, wadda rundunar sojin Sudan ke jagoranta, ranar Alhamis ta ce dakarunta sun daƙile hare-haren da mayaƙan RSF suka yi yunƙurin kaiwa a yankuna da dama na Arewacin Darfur.

Ci gaba da far wa fararen-hula

A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta zargi mayaƙan RSF da ci gaba da kai hare-hare kan fararen-hula, musamman a kusa da ƙauyen Abu Qamra, da zummar tursasa musu da kashe su da korar su, bayan sun samu mafaka a yankin sakamakon tun lokacin da aka kore su daga Al Fasher.

Majiyoyi a yankin sun ce mayaƙan RSF sun kai hare-hare a Abu Qamra da Ambro ranar Laraba, ko da yake RSF sun yi ikirarin kwace yankin shekaru biyu da suka wuce.

Sanarwar ta kara da cewa mayakan RSF sun kona daukacin kauyukan da ke yankin, da dabbobi da gidaje tare da aikata babban laifi na cin zarafin mazauna yankin.