Gwamnatin Jihar Katsina za ta shirya muƙabala tsakanin Yahya Masussuka da sauran Malaman Musulunci

“Domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, gwamnan Jihar Katsina Umaru Dikko Radda ya umarci Malam Yahya ya shirya kare kansa bisa zargin da ake masa a gaban majalisar malamai," in ji sanarwar.

By
Malam Yahaya Masussuka

Gwamnatin Jihar Katsina a arewacin Nijeriya ta ce za ta shirya muƙabala tsakanin Sheik Yahya Masussuka da ke da'awar a bi Ƙur’ani zalla da kuma sauran Malaman addinin Musulunci na jihar.

A wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar ya fitar a ranar Talata mai ɗauke da sa hannun daraktan yada labarai, Ibrahim Almu Gafai, ta ce za ta shirya muƙalabar ne bayan da sulhun da Fadar Sarkin Katsina ta yi wa Masussuka da Kungiyar Izala kwanakin baya ya ci tura.

Sanarwar gwamnatin ta ce tun da fari Ƙungiyar Izala ta kai ƙorafi kan cewa Yahya Masussuka abin da yake wa’azi a kai ya ci karo da Shari’ar Musulunci, inda shi ma Masussukan ya kai nasa ƙorafin cewa ‘yan izalar na cin mutuncinsa da barzanar kai masa hari.

Hakan ne ya sa gwamnatin ta yanke hukuncin tura matsalar gaban Sarkin Katsina don a yi musu sulhu, “inda Sarkin ya yanke hukuncin cewa babu wani malami da yake da damar yin wa’azi ko bin wata koyarwa da za ta ɓata ran Musulmai.”

Amma a sanarwar tata ta ranar Talata, gwamnatin Katsinan ta ce har yanzu ba a samu maslaha ba a kan lamarin.

“Domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, gwamnan Jihar Katsina Umaru Dikko Radda ya umarci Malam Yahya ya shirya kare kansa bisa zargin da ake masa a gaban majalisar malamai.

“Daga nan ne kuma za a tsara dokoki da tsare-tsare wadanda daga sannan duk wanda ya kauce musu to gwamnati za ta dauki matakin da ya dace a kan ko waye,” in ji sanarwar.

A karshe gwamnatin ta umarci al’umma da su yi hakuri saboda za a yi adalci a kan mas’alar.