Rikicin da ke ta’azzara ya tirsasa wa farar-hula fiye da 4,000 tserewa daga Kordofan a Sudan: MDD

Jihohin Kordofan uku sun shaida kazamin fada tsakani sojoji da mayakan RSF, wanda ya sanya dubban mutane barin yankunan.

By
Rikicin da ke tsakanin sojojin Sudan da RSF, wanda ya fara a watan Afrilun 2023, ya yi ajalin dubban mutane / Reuters

Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM) ta ce sama da fararen-hula 4,000 ne suka tsere daga jihohin Kudanci da Arewacin Kordofan a kudancin Sudan a cikin kwanaki uku da suka gabata sakamakon rashin tsaro da ke kara ta'azzara.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, Hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da rahoton korar mutane tsakanin 1,500 zuwa 2,500 daga Al-Kuweik a Kudancin Kordofan, baya ga mutane 375 daga Kadugli da wasu 495 daga Dilling da ke jihar tsakanin 27 zuwa 29 ga Disamba.

IOM ta ce mutanen da suka rasa matsugunin sun koma wurare daban-daban a jihohin Arewacin Kordofan, Kudancin Kordofan da White Nile.

A Arewacin Kordofan, kungiyar ta sami labarin tisasa wa mutane 1,020 gudun hijira daga kauyukan Um Taghirat da Al-Markha a yankin Jebrat Al-Sheikh saboda tabarbarewar yanayin tsaro, inda ta lura cewa sun gudu zuwa Omdurman da ke yammacin babban birnin Khartoum.

A ranar Lahadi, IOM ta sanar da cewa mutane 1,290 daga jihohin biyu sun rasa matsugunansu saboda dalilan rashin tsaro.

Jihohin Kordofan guda uku - Arewa, Yamma, da Kudu - sun fuskanci makonni na faɗa mai tsanani tsakanin sojoji da mayakan RSF wanda ya sa dubban mutane suka tsere.

Daga cikin jihohi 18 na Sudan, RSF na rike da iko da dukkan jihohi biyar na yankin yammacin Darfur, sai dai wasu sassan arewacin Darfur na Arewacin Darfur waɗanda har yanzu na ƙarƙashin ikon sojoji.

Sojojin Sudan, a gefe guda na riƙe da mafi yawan yankunan sauran jihohi 13 a kudu, arewa, gabas, da tsakiya, gami da babban birnin Khartoum.

Rikicin da ke tsakanin sojojin Sudan da RSF, wanda ya fara a watan Afrilun 2023, ya yi ajalin dubban mutane tare da korar miliyoyi daga matsugunansu.