| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Mai Bai wa Trump Shawara kan Addini tana shan raddi bayan ta kwatanta shi da Yesu Almasihu
Mai ba da shawara kan lamuran addini ta Shugaban Amurka Donald Trump tana fuskantar suka daga ko’ina a kafofin sada zumunta bayan ta kwatanta Trump da Yesu Almasihu a ranar Laraba.
Mai Bai wa Trump Shawara kan Addini tana shan raddi bayan ta kwatanta shi da Yesu Almasihu
Kalaman Paula White-Cain game da Donald Trump sun haifar da zargin sabo a tsakanin masu suka a shafukan yanar gizo. / AFP
3 awanni baya

Ana ci gaba da mayar da kakkausan martani a kafofin sada zumunta ga Mai Bai wa Trump Shawara kan Addini Paula White-Cain bayan ta kwatanta gwagwarmayar da Shugaba Donald Trump da na Yesu Almasihu (Annabi Isa AS) a wasu kalamai masu cike da ce-ce-ku-ce.

Mai ba da shawara kan lamuran addini ta Shugaban Amurka Donald Trump tana fuskantar suka daga ko’ina a kafofin sada zumunta bayan ta kwatanta Trump da Yesu Almasihu a ranar Laraba.

“Yesu ya koyar da darussa da dama ta hanyar mutuwarsa, binne shi, da kuma tashinsa. Ya nuna mana cewa kyakkyawan jagoranci da babban sauyi suna bukatar gagarumar sadaukarwa,” in ji Paula White-Cain.

“Kuma ya kai Shugaba Kasa, babu wanda ya sha wuya kamar yadda ka sha. Kusan hakan ya kusa yin sanadiyyar rayuwarka.

“An ci amanarka, an kama ka, kuma an yi maka kazafi. Wannan tsari ne da Jagoranmu kuma Mai Cetonmu ya nuna mana,” in ji ta.

“Amma hakan bai tsaya a nan ba a gare shi, kuma bai tsaya a nan ba a gare ka kaima.

“A ko da yaushe Allah yana da tsari. A rana ta uku, ya tashi, ya yi nasara a kan azzalumai, ya yi nasara a kan mutuwa da wuta da kuma kabari. Kuma saboda ya tashi, dukanmu mun san cewa za mu iya tashi. Kuma yallabai, saboda tashinsa daga matattu, kai ma ka sake mikewa,” in ji ta.

“Kuma na yi amanna cewa Ubangiji ya ce na gaya maka wannan — saboda nasararsa, kai ma za ka yi nasara a duk abin da ka sa hannunka,” kamar yadda ta shaida wa Trump.

Biyo bayan wadannan kalamai na nata, ma’abota shafukan sada zumunta sun yi wa Cain-White raddi mai zafi, inda wasu suka bayyana jawabin nata da “babban sabo” da kuma “rashin hankali.”